Muhuyi Magaji Rimin-Gado ya koka kan yadda wasu ke harin rayuwarsa

Muhuyi Magaji Rimin-Gado ya koka kan yadda wasu ke harin rayuwarsa

  • Rundunar 'yan sanda sun bayyana wasu bayanai kan Muhuyi, inda ya ce yana tsoron abinda zai biyo baya
  • Ya bayyana cewa, bayanan da aka bayar a kansa karya ne, kuma ba su da tushe ko kamshin gaskiya
  • Sai dai, rundunar 'yan sanda ta ce ta samo bayanan ne daga binciken da rundunar ta gudanar mai zurfi

Kano - Muhuyi Magaji Rimin-Gado, korarren Shugaban Hukumar Korafi da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ya nuna damuwa cewa wasu mutane na bibiyar rayuwarsa.

Muhuyi ya bayyana haka ne yayin magana da jaridar Daily Trust kan tuhumar bayanan karya da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta shigar a kansa, ya kara da cewa yana tsoratawa lafiyarsa.

Rimin-Gado yayin da ya ci gaba da cewa bai ji tsoron tuhumar da ake yi masa ba, ya yi zargin cewa tuhumar zalunci ce karara.

Read also

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

Ina tsoron abin da zai biyo baya: Muhuyi ya koka kan tuhumar rashawa da ake masa
Muhuyi Rimin-Gado | Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

A cewarsa, tuhumar da ake yi masa wani bangare ne na tsare -tsaren da ‘yan sanda ke yi na cutar da shi.

Ya kuma yi tambayar me ya sa 'yan sandan, wadanda tun farko ba su kama shi da laifi ba, a yanzu suka zo da laifin ba shi bayanan karya.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan da ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce rahoton da aka gabatar sakamakon bincike ne da rundunar ta gudanar.

Ya yi bayanin cewa hakan ya biyo bayan wata takarda da rundunar ta samu daga majalisar dokokin jihar Kani da babban akantan janar na jihar.

Majalisar jihar Kano ta dakatar da bincikar Muhuyi Rimingado

Majalisar jihar Kano ta dakatar da bincikar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, dakataccen shugaban hukumar karbar korafi da yaki da rashawa na jihar Kano.

Read also

NAF ta karyata rahoton biyan 'yan bindiga N20m don kada su harbo jirgin Buhari

Kwamitin wucin-gadi na majalisar a wata takarda da suka fitar a farkon makon nan, sun bukaci Rimin Gado da ya bayyana a gaban majalisar da karfe 12 na ranar Laraba, Daily Trust ta ruwaito.

Amma kuma a yayin jawabi ga manema labarai bayan bayyanarsa a gaban majalisar, sakataren kwamitin wucin-gadin, Abdullahi A. Bature ya ce zaman ba zai cigaba ba saboda kwamitin sun kafa tsarin bincikar Rimin Gado kamar yadda wasikar lauyansa ta bukata a ranar Laraba.

Duk da komawa APC, da alamu Fani-Kayode zai fuskanci fushin kotu saboda badakala

A wani labarin daban, Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Legas ta umarci tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, da ya biya tarar N200,000 saboda rashin halartarsa a sake gurfanar da shi da aka yi ko kuma ya fuskanci soke belinsa.

Gidan talabijin na Channels ya rahoto cewa, mai shari’a Daniel Osaigor ya ba da umurnin ne a ranar Laraba, yana mai cewa bayan ya duba fayil din kotun, ya lura da wasiku daban-daban guda biyar da ke neman a dage zaman a kan dalilan rashin lafiya.

Read also

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

Source: Legit.ng

Online view pixel