Bincike: Yadda Ministan Buhari yake amfani da kujerarsa yana yin abin da ya ga dama a mulki

Bincike: Yadda Ministan Buhari yake amfani da kujerarsa yana yin abin da ya ga dama a mulki

  • Ana zargin Ogbonnaya Onu da yin ba daidai ba a kan kujerar Ministan Tarayya
  • Bincike ya nuna Ministan ya rusa majalisun da ke sa ido a kan harkar ma’aikatu
  • Daga cikin zargin da ke kan Dr. Onu shi ne bada mukamai ga wanda bai dace ba

Abuja - A wani bincike na musamman da jaridar Punch tayi, an bankado irin badakalar da Dr. Ogbonnaya Onu yake tafka wa saboda damar da ya samu.

A karshen makon da ya gabata ne Ogbonnaya Onu ya nada ‘yan majalisar da ke kula da hukumomin da duk cibiyoyin da ke karkashin ma’aikatarsa.

Ministan ya yi hakan a lokacin da tsofaffin ‘yan majalisar ba su cika wa’adinsu ba. Ana zargin ya kore su ne saboda sun ki bada dama ya nada bara-gurbi a ofis.

Kara karanta wannan

Yadda shugaba a NIS ya yi shigan burtu ya kame jami'ansa dumu-dumu da rashawa

Da wannan mataki da Ministan ya dauka, ya dakatar da binciken da gwamnatin Buhari ta ke yi a ma’aikatarsa, sannan ya yi waje da duk masu adawa da shi.

Ogbonnaya Onu ya kinkimo dokar soji

Onu ya yi amfani da wata tsohuwar dokar soja ta shekarar 1977 wajen tsige ‘yan majalisar. Amma an yi masa raddi da cewa wannan doka ta dade da daina aiki.

A ka’ida ya kamata majalisar da ke sa ido a kan aikin hukuma ta yi shekara hudu ne, a maimakon uku. Amma duk da haka, Onu ya nuna karfin mulki, ya saba doka.

Ministan kimiyya
Dr. Ogbonnaya Onu da Buhari Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Hukumomin tarayyan da canjin ya shafa sun hada da; NBTI, NITR, NISLT, NITR, NAMBDA, NACETEM, NNMDA, NBBRI, NILEST, NARICT, da kuma PRODA.

Jaridar tace sauran sun hada da SHESTCO da FIIRO. Hukumomin da ba a taba ba su ne; NOTAP, ECN, SHESTCO), RMDC, NASENI, da hukumar nan ta RMRDC.

Kara karanta wannan

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

Onu yana yin katsalandan da wuce gona da iri

Sannan ana zargin Ministan na kimiyya da fasaha da yin katsalandan musamman a hukumomi irinsu PRODA wajen nadin sabon shugaba da ake shirin yi.

Shugaban kasa ya ja kunnen Ministan, amma sai aka sake ji ana zarginsa da cigaba da barin shugaban hukumar NITR a ofis duk da ya cika shekarun ritaya.

Duk da bai cancanta ba, Dr. Onu ya yi amfani da iko, wajen nada Chima Igwe, a matsayin shugaban hukumar FIIRO bayan cikar wa’adin Farfesa Gloria Elemo.

Majalisar da ke kula da FIIRO ba ta amince da hakan ba, domin ana zargin Igwe bai da takardu. Hakan ya sa Ministan ya ruguza majalisar ta Alhaji Ibrahim Gwarzo.

Ma’aikatar kimiyyar da Ministan ba su dauki waya da aka nemi jin ta bakinsu ba. Dr. Onu da shugaban kasa Muhammadu Buhari abokai ne, tun a zamanin ANPP.

SERAP za ta yi shari'a da Gwamnati

Kara karanta wannan

Rahoto: Sojoji 10 da wasu mutum 21 sun mutu a harin yan bindiga cikin mako ɗaya a Najeriya

A farkon makon nan ne aka ji cewa gwamnatin tarayya tayi kasafin biliyoyin kudi domin a san duk abin da jama’a suke yi a wayoyinsu da kuma kafar WhatsApp.

SERAP tace babu dalilin da zai sa hukumomin Gwamnati su san sirrrin Jama’a. Wannan ya sa kungiyar ta kai karar gwamnatin Muhammadu Buhari a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel