Kotu ta yanke wa wani bawan Allah da ya hallaka matarsa hukunci a jihar Kano

Kotu ta yanke wa wani bawan Allah da ya hallaka matarsa hukunci a jihar Kano

  • Wata kotu ta yanke wa wani mutumi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kama shi da laifin hallaka matarsa
  • Mutumin mai suna, Aminu Inuwa, ya musanta abinda ake zarginsa da shi, a cewarsa sam ba shine ya kashe matarsa ba
  • Amma masu gabatar da ƙara sun tabbatar da cewa shi ya aikata ƙisan bayan wani sa-insa ya haɗa shi da matar a ɗakin girki

Kano - Wata babbar kotu a jihar Kano, ranar Talata, ta yankewa wani mutumi, Aminu Inuwa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Daily Nigerian ta rahoto cewa kotu da kama mutumin da laifin kashe matarsa, Safara’u Mamman.

Malam Inuwa, wanda bamu gano haƙiƙanin shekarunsa ba, yana zaune ne a Gwazaye Quarters dake Ɗorayi babba, cikin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yadda Matar Aure Ta Zama Mai Aikin Goge-goge Don Tura Mijinta Makaranta A Kasar Waje, Bidiyon Ya Yadu

Kotu ta yanke hukunci
Kotu ta yanke wa wani bawan Allah da ya hallaka matarsa hukunci a jihar Kano Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Alkalin kotun, Mai shari'a Usman Na’abba, ya bayyana cewa hujjoji sun tabbatar da laifin wanda ake ƙara ba tare da tantama ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yaushe mutumin ya kashe matarsa?

Kafin yanke hukuncin, mai gabatar da ƙara Lamido Sorondinki, ya shaidawa kotu cewa mutumin ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Afrilu, 2019.

Sorondinki ya kara da cewa:

"Wanda ake zargin ya jiwa matarsa rauni a maƙogwaro da wukar daƙin girki lokacin da wata gardama ta haɗa su."
"Bayan ya tabbatar da ta mutu, sai ya haƙa mata kabari ya binne ta a wani karamin ɗaki da ba'a ƙarisa ba dake gidansa a Ɗorayi Babba."

Mai gabatar da ƙarar ya gabatar da shaidu 3 da kuma mutum 6 da aka nuna wa domin tabbatar da laifin wanda ake zargi, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wani Mutumi Ya Mutu a Ɗakin Hotel Bayan Ya Shiga da Wata Mace Zasu Ji Dadi

Shin mutumin ya amsa laifinsa?

A ɗaya ɓangaren kuwa, wanda aƙe ƙarar, Malam Inuwa, ya musanta maganar mai gabatar da ƙara, inda yace ba shine ya kashe matarsa ba.

Lauyan dake kare wanda ake ƙara, Mustapha Idris, ya gabatar da shaidu uku domin kare Malam Inuwa.

A wani labarin kuma kun ji yadda Wani mutumi ya hallaka matarsa mai kaunarsa da ɗan da suka haifa

Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin na zargin cewa mutumin ya samu taɓin kwakwalwa ne cikin kankanin lokaci.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah, yace an kai mutumin asibiti domin duba cikakkar lafiyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262