'Yan bindiga basu da tuta kamar Boko Haram da IPOB, ɓata gari ne kawai, Ministan Buhari, Lai Mohammed

'Yan bindiga basu da tuta kamar Boko Haram da IPOB, ɓata gari ne kawai, Ministan Buhari, Lai Mohammed

  • Ministan sadarwar ta al'adu, Lai Mohammed ya ce akwai banbanci tsakanin IPOB, Boko Haram da 'yan bindiga
  • Mohammed ya ce 'yan kungiyar IPOB da Boko Haram suna da manufofi sannan suna da tuta
  • Ya kara da cewa IPOB da Boko Haram suna kallubalantan Nigeria a matsayin kasar mai 'yanci yayin da 'yan bindiga bata gari ne kawai

Abuja - Ministan Sadarwa da Al'adu, Lai Mohammed ya ce yan bindiga da ke adabar yankin arewa maso yamma da wasu sassan arewa bata gari ne kawai.

Ya ce suna da banbanci da yan Boko Haram da yan kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biafra wato IPOB, domin suna da manufofi da tuta kamar yadda ya zo a ruwayar SaharaReporters.

Kara karanta wannan

Jarumin Gwamna El-Rufai ya bayyana abinda ke matukar tsorata shi

'Yan bindiga ba su da tuta kamar Boko Haram da IPOB, bata gari ne kawai, Ministan Buhari, Lai Mohammed
Ministan Sadarwa da Al'addun Nigeria. Lai Mohammed. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A cewarsa, 'yan bindigan bata gari ne kawai amma ba su jayayya da ikon Nigeria a matsayinta na kasa mai yanci ko hadin kanta kamar IPOB da Boko Haram.

Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, Ministan ya bayyana hakan ne yayin hira da aka yi da shi a shirin 'This Morning' a gidan talabijin na TVC a ranar Litinin.

Mohammed, daya daga cikin ministocin Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba dai-dai bane a rika kwatanta 'yan bindigan da IPOB da Boko Haram da ke manufofi ko alaka da addini.

Mohammed ya ce:

"Banbancin IPOB, Boko Haram shine a bangare guda, IPOB da Boko Haram suna da manufofi da suke son cimma, manufar cewa ba su son cigaba da zama 'yan Nigeria, yan bindiga ba su da tuta.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun damƙe dodanni biyu kan laifin aikata fashi da makami

"Yan bindiga ba su da tuta, bata gari ne kawai. Babu wani banbanci tsakanin yan bindiga da sauran bata gari sai dai sun fi su tsananta barna.
"Yan bindiga ba su taba cewa ba su yarda da kasancewar Nigeria a matsayin kasa ba, kawai bata gari ne masu laifi."

Ministan ya yi wannan kalaman ne a lokacin da wasu ke ta yin kiraye-kiraye na cewa shugaban kasa ya ayyana 'yan bindigan da makiyaya masu kisa a matsayin yan ta'adda.

A farkon watan Oktoba, Mohammed ya karyata zargin da ake yi na cewa shugaban kasa na yi wa 'yan bindiga sakwa-sakwa yana mai cewa gwamnati bata raga wa duk wani mai laifi.

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A wani rahoton, wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun kashe sojoji, sun raunata janar, sun yi awon gaba da motocin soji

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel