Boko Haram sun kashe sojoji, sun raunata janar, sun yi awon gaba da motocin soji
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari jihar Borno, inda suka hallaka sojoji da dama tare da sace makamai
- Harin ya faru ne a ranar Lahadi a wani gari da ke tsakanin jihar ta Borno da kuma makwabciyarta Yobe
- Garuruwa a yankin na ci gaba da fuskantar munanan hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP
Borno - Wasu 'yan ta'adda daga kungiyar Boko Haram da ke hade da kungiyar ISWAP a ranar Lahadin da ta gabata sun kai hari kan wata rundunar soja da ke a yankin Ngamdu, garin kan iyaka tsakanin Borno da Yobe
A wannan mummunan harin, sun kashe sojoji sama da 6 kamar yadda majiyoyin soji suka shaida wa SaharaReporters.
Ngamdu gari ne a karkashin karamar hukumar Kaga ta jihar Borno kuma kusan kilomita 100 zuwa babban birnin Maiduguri.
SaharaReporters ta tattaro cewa 'yan ta'addan sun shigo da a kalla manyan bindigogi 10 kuma ba za a iya kirga yawansu ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya ta ce kimanin sojojin Najeriya shida aka kashe, yayin da wasu da suka hada da Birgediya Janar da ke kula da sansanin suka jikkata.
Maharan sun kuma tafi da motar atisaye ta sojoji, makamai daban-daban da alburusai.
Harin na zuwa ne 'yan makwanni kadan bayan da maharan suka kashe sojoji sama da 25 wadanda su ma suke kan aikin sintiri a yankin Monguno na jihar Borno.
Yankin Borno da Yobe a Arewa maso gabas na daga cikin jihohin da suke fama da matsalar Boko Haram, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a yankin.
Duk da irin munanan hare-haren da ake yawan samu daga 'yan ta'adda a yankin, sojojin Najeriya na ci gaba da samun nasara a kan 'yan Boko Haram da ISWAP.
A shekarar nan ta 2021, an samu dubban 'yan ta'addan Boko Haram da suka mika kansu ga jami'an soji biyo bayan mutuwar shugabansu, Abubakar Shekau.
Boko Halal: Yadda aka kirkiri wani littafi mai yaki da akidun Boko Haram a jihar Borno
A kokarin dakile Boko Haram, Gidauniyar Allamin Foundation for Peace, wata kungiya mai zaman kanta (NGO) da ke Maiduguri, jihar Borno, a ranar Lahadi, 10 ga Oktoba, ta gabatar da littafi mai suna ‘Boko Halal’, littafin da aka rubuta don yakar akidun masu tsatsauran ra’ayi.
Da farko an rubuta littafin Boko Halal da harshen Turanci amma yanzu an gajartashi kana da fassara shi zuwa harsunan Hausa da Kanuri, HumAngle ta ruwaito.
Sunan littafin, wanda ke nufin ilimin Boko ba haramun bane, kai tsaye yana kalubalantar tsauraran akidun ta'addanci na Boko Haram.
Asali: Legit.ng