'Yan sanda sun damƙe dodanni biyu kan laifin aikata fashi da makami
- Yan sanda a jihar Ondo sun kama wasu dodanni biyu kan fashi da makami
- Dodannin sun yi wa wani fashin N370,000 da wayarsa da salula da rigarsa
- Yan sandan sun ce dodannin biyu na tsare kuma za a kai su kotu bayan bincike
Jihar Ondo - Rundunar 'yan sandan Nigeria reshen jihar Ondo ta yi nasarar cafke wasu dodanni biyu kan yi wa mazauna unguwar Melege a karamar hukumar Owo ta jihar fashi.
An kama dodannin biyu da aka ce sunansu Sheriff Ojo da Muhammed Lukman bayan sun yi wa wani Adinoyi Mohammed fashin N370,000 da wayarsa ta salula, rahoton Vanguard.
Ruwayar jaridar Daily Trust ya ce mai magana da yawun 'yan sandan jihar Ondo, Funmi Odulami ta tabbatar da afkuwar lamarin.
A cewar Odulami:
"Mutanen biyu da ake zargi wadanda ke gabatar da kansu a matsayin dodanni, sun raunata wani Adinoyi Mohammed da adda, suka kwace masa N370,000 da wayansa na N32,000 da rigarsa ta N2,500.
"Sun kuma raunata mahaifin wanda suka yi wa fashin mai suna Saliu Ajayi kafin barin wurin da abin ya faru amma daga baya jami'an 'yan sanda sun gano su a garin.
"An kwato adduna biyu, guru da layyu da kayan dodanni a hannunsu bayan kama su kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya su girbi abin da suka shuka da zarar an gama bincike."
Kakakin 'yan sandan ta kara da cewa ana cigaba da bin sahun wasu dodannin da suke tsere kamar yadda ya zo a ruwayar Tribune.
Me ya yi zafi: Saurayi ya bi buduwarsa har wurin alibidi ya buɗe wa baƙi wuta da bindigarsa
A wani rahoton, Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo a ranar Talata ta tabbatar da kama wani mutum wanda ake zargin ya bude wa baki wuta a wani alibidi da aka yi a Oba Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta kudu maso yamma da ke jihar.
Kamar yadda Punch ta ruwaito, a ranar Asabar ana tsaka da shagalin ne wanda ake zargin ya afka wurin ya hau harbe-harbe a cikin bainar jama’a bayan ya hango budurwar sa tare da wani saurayin.
Duk da dai babu wata asarar rai da aka yi, baki da dama sun samu miyagun raunuka yayin da kowa ya ranta a na kare.
Asali: Legit.ng