Kallo ya koma sama: Bidiyon ango ɗan Nigeria sanye da siket yana tiƙa rawa a ranar aurensa ya ɗauki hankula

Kallo ya koma sama: Bidiyon ango ɗan Nigeria sanye da siket yana tiƙa rawa a ranar aurensa ya ɗauki hankula

  • Mutane da dama sun sha mamaki akan yadda wani ango ya sanya buje a ranar daurin aurensa
  • Bayyanar bidiyon angon sanye da buje yayin da yake kwasar rawa ya sa mutane da dama nishadi
  • Mutane da dama a kafafen sada zumunta sun yi ta caccakar shigar ta shi, wasu su na cewa sabon salo ne

Jihar Edo - Wani matashi ya bawa mutane da dama mamaki yayin da wasu su ka dinga kwasar nishadi bayan ya yi wata shiga ta daban a ranar aurensa.

A cikin wani bidiyo da @instablog9ja ta wallafa, an gano mutumin sanye da 'buje' da safa fari. Sannan ya saka suit da tie.

An yi shagalin bikin ne a jihar Edo inda mutane da dama ba su taba ganin irin shigar ta shi ba.

Read also

Yadda jami'an tsaro suka yi wa likita da majinyata lugude a asibitin Abuja

Kallo ya koma sama: Ango ya bayyana sanye da buje a ranar aurensa
Ango ya bayyana sanye da buje a ranar aurensa. Hoto: @instablog9ja
Source: Instagram

Akwai wadanda su ka dinga dariya bayan ganin bidiyon na shi wanda ya dinga kwasar rawa sanye da bujen a jikin sa.

Duk da dai wasu sun ce shigar ta mutanen Scotland ce, da yake bujen da ya sa yana da tattara sannan ya sa doguwar farar safa a kafar sa.

Cikin alfahari ya bayyana sanye da buje

Bayan sa bujen ya sanya riga wacce ta dace. Kuma ya bayyana a wurin bikin cike da alfahari tare da zankadediyar amaryarsa.

Nan da nan mutanen da su ka halarci daurin auren su ka zagaye su su na manna mu su kudade. Duk da bujen da ke sanye a jikin sa, har wani salon rawar ‘gbese’ ya yi. Nan da nan aka fara ihu a wurin, alamar ya kayatar.

Read also

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

Mutane kimanin 54,000 sun latsa cewa bidiyon ya birge su sannan fiye da 2,000 sun yi tsokaci a kai.

Ga bidiyon a kasa:

Cikin tsokacin da bidiyon ya samu akwai na wata ha_lee.ma, inda ta ce:

“Ina son yadda mutane da dama a kasar nan su ke nishadantar da mu.”

Acg.gram ya ce:

“Scotland a cikin Benin.”

Official_bobby_fredrick ya ce:

“Wannan shigar ‘yan kasar Scotland ne. Yanzu fa sai mutane su fara yaba ma sa.”

Official_eddy92 ya ce:

“Wannan fa ba buje bane, ana kiran sa da Celt, wata shigar gargajiya ce ta mazan Celt.”

Taviaogun ya ce:

“Daga Scotland ya ke halan, saboda haka mazan kasar su ke shigar su.”

Broda_henry ya ce:

“Wannan sabon salo ne, ina son yadda ya kirkiro sabon abu.”

Source: Legit.ng

Online view pixel