Yadda jami'an tsaro suka yi wa likita da majinyata lugude a asibitin Abuja

Yadda jami'an tsaro suka yi wa likita da majinyata lugude a asibitin Abuja

  • Wasu 'yan sanda sun shiga asibitin gwamnati na Maitama da ke Abuja inda suka yi wa likita duka tare da wasu majinyata
  • Kamar yadda likita Dr. Adaeze ta sanar, an duba dan sandan sai dai kuma bai gamsu ba, lamarin da yasa tace ya je wani asibitin
  • A take ya dinga dukan ta tare da hadawa da wasu majinyata biyu wadanda suka kawo mata dauki kuma ya kira abokinsa ya taya shi dukan

Abuja - An zargi wasu jami'an tsaro da yi wa wata likita da wasu majinyata mugun duka a babban asibitin Maitama da ke Abuja a ranar Alhamis.

Dr. Okpalla Adaeze, daya daga cikin wadanda jami'an tsaron suka nada, ta sanar da Daily Trust cewa wannan cin zarafin aikin wani dan sanda ne da ya zo a duba shi.

Kara karanta wannan

Kallo ya koma sama: Bidiyon ango ɗan Nigeria sanye da siket yana tiƙa rawa a ranar aurensa ya ɗauki hankula

Yadda jami'an tsaro suka yi wa likita da majinyata lugude a asibitin Abuja
Yadda jami'an tsaro suka yi wa likita da majinyata lugude a asibitin Abuja. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ta ce hakurin sa ya kare ne lokacin da daya daga cikin dakunan suka ki karbarsa, Daily Trust ta ruwaito.

Adaeze ta ce ba ta kula shi ba saboda bangaren kula da marasa lafiyan da suka isa asibitin da farko sun kula da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Da gaggawa na sanar da su cewa ba su da matsala da ayyukan gaggawa. Na kara da yi musu bayanin cewa tunda an duba shi kuma bai gamsu da hakan ba, ya je wani wuri. Kawai sai ji na yi ya fara duka na," Adaeze tace.

Ta kara da cewa, sai da wasu majinyata suka shiga lamarin kafin ta samu ta gudu, kuma hakan yasa ya mayar da masifarsa kan wasu majinyata biyu.

Adaeze, wacce ta gano sunan daya daga cikin jami'an da Ogochie Kingsley, ta ce daga bisani ya kira abokinsa dan sanda wanda ya isa asibitin da bindigogi biyu.

Kara karanta wannan

Ba guduwa zan yi ba: Sheikh Zakzaky ya zargi gwamnatin Buhari da hana shi sakat

"Da farko abokin ya yi ikirarin shi jami'in DSS ne kuma ya bukaci Kingsley ya nuna masa wadanda suka kai masa farmakin. Ya nuna wasu majinyata 2 saboda ni na boye. Abokin ya yi amfani da kasan bindiga inda ya dinga dukan majinyacin da aka yi wa aiki."

Jamilu Bala Muhammad, daya daga cikin majinyatan da aka duka, ya zage inda ya jibgi dan sandan.

Ya ce 'yan sanda daga ofishinsu na Maitama daga bisani sun shiga lamarin inda suka damke tare da kulle maharan.

"Yayin da muka isa ofishin, wanda ke ikirarin zama jami'in DSS ne ya ce dan sanda ne shi, kuma ya bukaci Kingsley da ya sanar da cewa majinyatan ne suka kai masa farmaki da adda tare da kaca," yace.

Sojoji 4 sun sheka lahira, 1 ya jigata yayin arangama da 'yan ISWAP a Borno

A wani labari na daban, a kalla sojoji hudu ne suka rasa ran su a ranar Talata yayin bankado harin da mayakan ISWAP suka kai garin Ngamdu, wani gari da ke tsakanin iyakar jihohin Yobe da Borno.

Kara karanta wannan

Kaduna: Kotun sharia ta umurci a yi wa magidanci bulala 80 saboda yi wa matarsa ƙazafi kan haihuwar ɗansu na 6

PRNigeria ta tattaro cewa, majiya mai karfi daga rundunar ta ce harbin ya samu hafsan sojan ne yayin da ya ke kokarin bai wa bataliyarsa kariya daga 'yan ta'addan.

An ruwaito cewa hafsan sojan ya samu miyagun raunika. Amma kuma an kai shi asibitin sojoji inda ya ke samun sauki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel