Sojoji 4 sun sheka lahira, 1 ya jigata yayin arangama da 'yan ISWAP a Borno

Sojoji 4 sun sheka lahira, 1 ya jigata yayin arangama da 'yan ISWAP a Borno

  • Dakarun soji hudu ne suka rasa rayukansu yayin da hafsan soja 1 ya samu miyagun raunika a Borno
  • Sojojin sun rasu ne yayin da suka yi kokarin tare 'yan ISWAP da suka zagaya za su shiga sansanin sojin Ngamdu
  • Hafsan sojan cike da kwarewa tare da jarumta ya yi yunkurin bai wa sojojinsa kariya, lamarin da yasa harsasai suka same shi

Borno - A kalla sojoji hudu ne suka rasa ran su a ranar Talata yayin bankado harin da mayakan ISWAP suka kai garin Ngamdu, wani gari da ke tsakanin iyakar jihohin Yobe da Borno.

PRNigeria ta tattaro cewa, majiya mai karfi daga rundunar ta ce harbin ya samu hafsan sojan ne yayin da ya ke kokarin bai wa bataliyarsa kariya daga 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi wa tsoffin sojojin Biyafara 102 afuwa, ya amince da biyansu kudin sallama

Sojoji 4 sun sheka lahira, 1 ya jigata yayin arangama da 'yan ISWAP a Borno
Sojoji 4 sun sheka lahira, 1 ya jigata yayin arangama da 'yan ISWAP a Borno. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

An ruwaito cewa hafsan sojan ya samu miyagun raunika. Amma kuma an kai shi asibitin sojoji inda ya ke samun sauki.

"Yayin da dakarun suke musayar wuta da 'yan ta'addan ISWAP, wasu daga cikin 'yan ta'addan sun lallaba tare da yunkurin shiga sansanin sojojin da ke Ngamdu ta baya. A wannan lokacin ne hafsan sojan tare da bataliyarsa suka tunkare su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Sai dai cike da rashin sa'a, sojoji hudu sun samu miyagun raunika wanda daga baya suka ce ga garin ku," a cewar majiyar
"Hafsan sojan da ya yi yunkurin bai wa dakarun kariya, ya samu raunika sakamakon harin. Sai dai yanzu haka ya na samun kulawa a asibiti. Cike da nasara dakarun sun dakile harin," majiyar ta ce.

Kwanton bauna: Soji sun yi wa mayakan ISWAP raga-raga a hanyarsu ta kai farmaki Ngamdu

Kara karanta wannan

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

A wani labari na daban, jiragen yaki biyu masu saukar angulu na rundunar sojin saman Najeriya, NAF, a ranar Talata sun bankado mummunan farmakin da 'yan ta'adda suka kai garin Ngamdu, garin da ke da iyaka da jihohin Yobe da Borno.

PRNigeria ta tattaro cewa 'yan ta'addan sun yi kokarin kai farmaki sansanin sojoji da ke yankin kafin dakarun sojin su bankado mugun nufin.

An gano cewa mayakan ta'addancin Islamic State of West Africa Province (ISWAP) ne suka shirya farmakin kuma jiragen sojojin tare da taimakon sojin kasa da ke sansanin Ngamdu suka dakile.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel