Kaduna: Kotun sharia ta umurci a yi wa magidanci bulala 80 saboda yi wa matarsa ƙazafi kan haihuwar ɗansu na 6
- Alkalin kotu shari'a ya bada umurnin a yi wa wani magidanci bulala guda 80 a Kaduna
- Hakan ya biyo bayan zargin matarsa da ya yi na cewa ta kawo masa cikin shege gidansa ne
- Kotun ta umurci a yi wa magidancin bulalan ne bayan ta bashi damar ya kawo hujja ko rantsuwa amma ya ki
Kaduna - Wata kotun shari'a da ke zamanta a Magajin Gari, Jihar Kaduna, a ranar Laraba ta bada umurnin a yi wa wani treda mazaunin Bakin Dogo, Abdulhamid Yakubu bulala 80.
Kotun ta yanke wannan hukuncin ne saboda Yakubu ya musanta cewa shine mahaifin dansu na shida da matarsa ta haifa kamar yadda NewsWireNGR ta ruwaito.
A cewar ruwaiyar jaridar NewsWireNGR, Alkalin kotun, Murtala Nasir, ya tabbatar da cewa dan da aka haifa na Yakubu ne.
Nasir ya umurce shi ya cigaba da daukan dawainiyar dukkan yaransa shida.
Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ta ruwaito cewa a watan Satumba, Yakubu ya maka matarsa Maryam Muhammad a kotu, yana zargin cewa ta ci amanarsa na aure kuma cikin da ta ke dauke da shi ba nasa bane.
NAN ta kuma ruwaito cewa an bawa wanda ya yi karar zabin yin rantsuwa kan cewa ba shine mahaifin dan ta matarsa ta haifa ba ko ya kawo shaida da ke nuna dan ba nasa bane amma ya ki yin hakan.
Ma'auratan sun shafe shekaru 21 suna zaman aure kuma Maryam Muhammad ta haifi dansu na shida da aka saka wa suna Abdulazeez.
A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu
A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.
Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.
Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng