Sana'o'i 6 Da Za Ku Iya Koya a 2024 Don Kaucewa Fadawa 'Talauci'

Sana'o'i 6 Da Za Ku Iya Koya a 2024 Don Kaucewa Fadawa 'Talauci'

  • A yayin da aka shiga shekarar 2024, Legit Hausa ta yi nazari kan wasu fasahohi da mutum zai koya don neman aiki tare da samun kudi da su
  • La'akari da cewa aikin gwamnati ya yi karanci, dole akwai bukatar 'yan Najeriya su nemi wasu hanyoyin samun kudaden shiga
  • Tun daga fasahar bincike da tattara bayanai zuwa ilimin fasahar kirkirar labarai na rubutu ko bidiyo, akwai fasahohi da za su kawo kudi a 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Akwai manyan fasahohi da mutum zai koya a yanar gizo wadanda ake neman masu kwarewa kan su a fadin duniya, kuma ana samun kudi masu yawa.

A halin yanzu da samun aikin gwamnati ya yi wahala, da tabarbarewar tattalin arziki a kasar, akwai bukatar mutum ya zama mai fadada tunani da iliminsa don samun kudi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a wani babban kanti a jihar Nasarawa, sun kashe mutum 4

Fasahohi 6 na samun kudi a 2024
Legit Hausa ta yi nazari kan wasu ilimin fasahohi 6 da mutum zai koya don samun kudi a 2024
Asali: Getty Images

Rahotan Daily Trust ya yi bayani kan wasu manyan sana'o'in fasaha da mutum zai koya don yaki da talauci a shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike da sarrafa bayanai - 'Data analysis'

Ilimin sana'ar sarrafa bayanai ta shafi nemo bayanai, yin nazarinsu da sake rubuta su a saukake da kuma yin amfani da bayanan don warware matsalolin kasuwanci.

Manyan kamfanoni sun dogara da bayanai don tafiyar da kasuwancinsu, suna bukatar mai ilimin tattara bayani ya yi masu wannan aikin, cewar makarantar kasuwanci ta Harvard.

Kana bukatar ilimin sarrafa manhajar Microsoft Excel, Google Sheets, SQL, Tableau, R, ko Python don gudanar da wannan sana'ar.

Ilimin kirkirar manhajoji - 'Software development'

Wannan ilimin fasahar ya kunshi gina manhaja, kula da ita, da kuma habbaka yadda take aiki dai dai da zamani.

A halin yanzu, manya da kananan kafanoni na bukatar shafuka a yanar gizo don tallata hajojinsu, idan kana da ilimin kirkirar manhajoji, za ka samu kudi masu yawa.

Kara karanta wannan

2024: Tinubu ya fadi biliyoyin naira da zai kashe wajen dawo da shirin ciyar da dalibai abinci

Masu gina manhajoji na iya amfani da kayan aikin kamar Git, Docker, Jenkins, ko Kubernetes, kuma kila su san ilimin harsunan 'coding' kamar Python, Java, ko C++.

Tallace-tallace a yanar gizo - 'Digital marketing'

Wannan fasahar kasuwancin ya shafi kirkira da aiwatar da dabarun kasuwanci a yanar gizo don tallata hajoji ga mutane.

Kwarewa a sanin halayyar mutane a yanar gizo, abin da suke bukata, yadda za ka samun yardarsu, ya na kai wa mutum ya samu kudade masu yawa wajen tallata kaya a yanar gizo.

Ilimin rubuce-rubuce - 'Copywriting'

Wannan ilimin fasahar na bukatar mutum ya zamo mai yin rubuce-rubuce a shafukan jarida, kafofin watsa labarai na zamani ko sakon 'email'.

Ana ci gaba da samun karuwar gidajen jaridu a yanar gizo da ke neman wadanda suka kware a tsara rubutu da zai ja hankalin mutane.

Manhajoji irin su Grammarly, Hemingway, ko CoSchedule na taimaka wa mai fasahar rubutu don inganta kyawun labarin da ya rubuta.

Kara karanta wannan

"Sun ce zai kammalu a Disamba": Iyali sun kadu bayan ganin katafaren gidansu a kauye

Ilimin sarrafa na'ura a yanar gizo - 'Machine learning'

Wannan ilimin na kawo kudi, domin kamfanoni na neman kwararru da za su iya sarrafa tunanin na'ura mai kwakwalwa wajen tattara bayanai da yin hasashen abubuwa.

Masu son koyon wannan ilimi za su koyi yadda ake amfani da manhajar TensorFlow, PyTorch, ko Scikit-learn.

Kirkirar labarai zuwa rubutu ko bidiyo - 'Content creation'

Wannan fasahar tana bukatar mutum ya zamo mai nazari don samar da labari da zai gamsar da mai karatu ko kallonsa.

Ilimin ya shafi sarrafa tunani don jan hankalin mutane da nufin samun tallace-tallace ko isar da wani sako cikin salo na burgewa.

Abin da ha jawo turawa suna daina saka hannun jari a Najeriya

A wani labarin na daban, kungiyar CNPP ta ja hankalin shugaba Bola Tinubu kan yawaitar raguwar turawan da ke yin kasuwanci a cikin Najeriy.

Kungiyar ta ce rashin samun turawan da za su saka hannun jari a Najeriya zai jawo babbar illa ga tattalin arzikin kasar, don haka ta ba da shawara kan wata mafitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel