Canjin Naira da Wasu Matsalolin Tattalin Arziki 9 da ‘Yan Najeriya Su ka Fuskanta a 2023

Canjin Naira da Wasu Matsalolin Tattalin Arziki 9 da ‘Yan Najeriya Su ka Fuskanta a 2023

  • Tattalin arzikin Najeriya ya shiga wani irin mawuyacin hali a shekarar nan da za a fita watau 2023
  • A shekarar bana kuma an yi fama da jarabar tsadar kaya musamman abinci baya ga hauhawan farashi
  • Bayan tsadar da kaya suke yi kullum a kasuwa, an yi karancin kudi saboda canza N200, N500 da N1000

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Shekarar nan ta 2023 ta za da kalubale masu yawa ga duniya wanda hakan ya shafi mutanen Najeriya sosai.

Godwin Emefiele ya kawo sababbin kudi da yake Gwamnan CBN, canjin kudin ye jefa al’umma a tsaka mai wuya.

Tattalin arziki
Matsin lambar tattalin arziki a 2023 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Legit ta bibiyi irin wahalhalun da aka fuskanta a wannan shekara:

Kara karanta wannan

Mafi munin sata da rashin gaskiyar da aka yi a lokacin mulkin Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Canjin kudi

An fara shekarar nan ne da wahalar canza takardun Nairori da aka yi. Bankin CBN ya fito da sababbin N200, N500 da N1000 da samunsu ya yi wahala.

Wannan tsari da Godwin Emefiele ya kawo da nufin inganta tattalin arziki da tsaro ya azabtar da ‘yan kasuwa da jawo karancin kudi da tsadar kaya.

2. Kayyade kudin da za a cire

Daily Trust ta ce tsarin da aka kawo na takaita adadin kudin da za a iya cirewa a kowace rana ya rage yawan kudin da su ke yawo a fadin Najeriya.

Babban bankin CBN ya ce mafi yawan kudin da aka buga sun daina shiga bankuna. A dalilin haka aka sha wahala, masu POS su ka rika lafta ladansu.

3. Hauhawar farashin kaya

Alkaluman NBS sun nuna hauhawar farashin kaya ya kai 28.2% a shekarar nan, wannan ne mafi munin tsadan da kaya suka yi a cikin shekaru 20.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin tarayya ta fara rabawa talakawa N20,000

4. Abinci ya yi tsada

Jama’a sun gamu da kalubalen tsadar abinci sosai a bana saboda dalilan da su ka kunshi rashin tsaro, tsadar kayan gona da daukewar ruwan sama.

Rahoton ya ce wannan ya sake jefa miliyoyin mutanen Najeriya a kangin talauci.

5. Karin ruwa a kan bashi

Shugabannin CBN sun kara ruwa da ke kan bashi zuwa 18.75% a kokarin ganin an yi maganin tashin farashi, hakan ya wahalar da ‘yan kasuwa.

6. Karya darajar Naira

A shekarar nan bankin CBN ya saki farashin kudin kasar waje a hannun ‘yan kasuwa da sunan daidaita farashi, a karshe Naira ta yi rugu-rugu.

7. Tsadar man fetur

Da Bola Tinubu ya karbi mulki man fetur ya tashi daga kasa da N200 zuwa fiye da N600. Sabuwar gwamnati ta sanara da janye tallafin fetur a yanzu.

8. Tsarin kwastam

Ana da labari canjin da aka samu wajen shigo da kaya zai jawo tsadar kaya. Kwastam ta kara kudin da ake karba kafin kaya su shigo Najeriya.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta fara tuhumar wasu manyan ministocin Buhari kan badakalar naira biliyan 187

9. Litar Dizil ta tashi

Baya ga fetur, ana da labari dizil ya kara kudi a 2023, hakan ya taimaka wajen tsadar kayayyaki saboda kudin dakonsu a manyan motoci ya karu sosai.

10. Rufe iyakar Nijar

Ana da labari mutane da-dama musamman 'yan kasuwa sun koka a kan yadda rufe iyakokin Najeriya da Nijar bayan juyin mulki ya kawo masu cikas.

Abinci zai kara tsada a 2024

Dr. Abubakar Sani Abdullahi ya tabbatar mana yanzu babu isasshen abinci kuma alamu na nuna tsadar da za a fuskanta a 2024 ta fi ta bana.

Masanin tattalin arzikin noman ya ce tallafin fetur da aka cire ya sa manoma ba su iya zuwa ganoki sannan akwai matsalar tsaro a jihohi.

Kwararren manomin kuma malami a jami'ar ABU Zariya ya ce kungiyoyi masu zaman kansu da gwamnati suna rububin amfanin gona.

Asali: Legit.ng

Online view pixel