Yahaya Bello: Jerin Tsofaffin Gwamnoni da Suka Yi Wa EFCC Turjiya a Lokacin Cafke Su

Yahaya Bello: Jerin Tsofaffin Gwamnoni da Suka Yi Wa EFCC Turjiya a Lokacin Cafke Su

Har yanzu ana tattauna irin dambarwar da aka tafka a lokacin da jami'an hukumar EFCC suka je cafke tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu, a gidansa da ke Abuja.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

An ruwaito cewa wasu jami’an ‘yan sanda da magoya bayan tsohon gwamnan ne suka yi wa jami’an EFCC cikas wajen kama shi duk da sun mamaye gidan nasa.

Fiye da sa’o’i 10, tsohon gwamnan, wanda aka fi sani da “Farin zaki”, ya gaza fita daga gidansa har sai da magajinsa Gwamna Ahmed Ododo ya kai masa daukin gaggawa.

Yahaya Bello, Rochas Okorocha, Ayodele Fayose, Willie Obiano da EFCC ta kama
Jerin tsofaffin gwamnonin da suka kwashi 'yan kallo da EFCC a lokacin kama su. Hoto: @GovAyoFayose, @OfficialGYBKogi, @realRochas
Asali: Twitter

Kamar yadda EFCC ta bayyana a ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilu, ta saka sunan Yahaya Bello a jerin wadanda take nema ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Badakalar $720, 000: Yadda muka yi da tsohon gwamna Yahaya Bello Inji Shugaban EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar imagireshan (NIS) da hukumar DSS sun sanya tsohon gwamnan a jerin wadanda suke bin diddiginsa tare da niyyar kama shi a duk inda aka hadu da shi.

Yahaya Bello dai ba shi ne tsohon gwamna na farko da hukumar EFCC ta sha wahala kafin ta kama shi ba. Akalla akwai wasu uku da suka nunawa hukumar jan ido.

"EFCC, ga ni na zo"- Fayose

A yayin da yake samun kariya a matsayinsa na gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya kwana da sanin cewa EFCC za ta nemi kama shi a idan wa’adinsa ya kare.

A ranar 16 ga Oktoba, 2018, kwana guda kafin karewar mulkinsa, Fayose ya mika ragamar jihar ga shugaban ma’aikatan gwamnati inda ya tafi Abuja domin mika kansa ga hukumar EFCC.

Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya mika kansa ga hukumar EFCC
Yadda Fayose ya mika kansa ga hukumar EFCC. Hoto: @GovAyoFayose
Asali: Twitter

Fayose ya nuna wa hukumar jan indo a wannan ranar, inda ya sanya riga mai dauke da rubutu “EFCC, ga ni na zo,” kuma ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

Dala a babbar riga: Hadimin Atiku ya dage, yana so hukumar EFCC ta binciki Ganduje

Tsohon gwamnan ya je ofishin EFCC da wata jaka mai dauke da kayan bacci da matashin kai, inda ya ce a shirye yake EFCC ta tsare shi muddin haka suke so.

Manyan ‘yan siyasa da suka hada da Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas a lokacin, da Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, suka yi wa Fayose rakiya zuwa ofishin.

Bayan ‘yan kwanaki EFCC ta gurfanar da Fayose a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 11 da suka hada da halasta kudaden haram da satar kudi har Naira biliyan 6.9. Har yanzu ana shari'ar.

Kalli bidiyon tsohon gwamnan da Daily Trust ta wallafa a nan kasa:

"Sun zo za su harbe ni" - Okorocha

Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo, na daya daga cikin wadanda aka kai ruwa rana su a lokacin jami'in hukumar EFCC suka yi kokarin kama shi.

A ranar 24 ga Mayu, 2022, jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa suka kai farmaki gidan tsohon gwamnan da ke unguwar Maitama a Abuja da nufin cafke shi.

Kara karanta wannan

Gwamna Ododo ya hana a cafke Yahaya Bello? Gaskiya ta bayyana

Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha da jami'an EFCC suka mamaye gidansa
Yadda EFCC ta kama tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha. Hoto: Rochas Okorocha
Asali: Twitter

Bayan an kwashe awanni tana jira, EFCC ta fara fasa kofar gidan. A lokacin ne Okorocha ya fara daukar bidiyon kai tsaye a shafin sa na Facebook domin duniya ta ga halin da yake ciki.

Daga karshe dai an kama Okorocha a wannan rana bayan da jami’an EFCC suka kutsa cikin gidan ta rufin dakinsa.

Jami’an suka kuma tarwatsa magoya bayan tsohon gwamnan wadanda suka yi taruruwa a gidan domin hana su fita da shi.

Daga baya EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa tuhumar sa da laifuka 17 na satar naira biliyan 2.9. Har yanzu ana shari'ar.

Kalli bidiyon gidan wanda TVCNews ya wallafa a nan:

EFCC ta kama Obiano a Legas

An kwashi 'yan kallo sosai a lokacin da hukumar EFCC ta je kama tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a ranar 16 ga Maris, 2022.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Hukumar NIS ta umarci jami'ai su sanya ido kan motsin tsohon gwamna

A wannan ranar ne tsohon gwamnan ya halarci bikin rantsar da magajinsa, Charles Soludo. Amma duk da hakan, EFCC ta yi ikirarin cewa Obiano na kokarin guduwa ne zuwa Amurka don kar a kama shi.

EFCC ta kama Willie Obiano a kan hanyarsa ta zuwa birnin Houston na kasar Amurka
Yadda EFCC ta kama tare da tsare tsohon Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra. Hoto: Willie Obiano
Asali: Facebook

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta rubutawa hukumar NIS wasika a watan Nuwamba 2021 domin ta saka ido kan Obiano tare da sanar da su duk lokacin da zai bar kasar.

Jami’an EFCC sun kama Obianoa ne da misalin karfe 8:30 na dare a lokacin da yake shirin shiga jirgin da zai bar Najeriya zuwa birnin Houston na kasar Amurka.

A watan Janairun 2024, an kama tsohon gwamnan da laifin satar sama da Naira biliyan hudu. Har yanzu dai shari’ar tana gaban alkali Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kalli bidiyon tsohon Gwamna Obiano a hannun EFCC wanda shafin Gist ya wallafa:

Ondo 2024: Masu neman takara a PDP

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta yi barazanar hada-kai da sojoji domin kamo tsohon gwamnan APC

A wani labarin, Legit Hausa ta tattaro maku bayani kan jerin wasu manyan masu neman takarar kujerar gwmanan jihar Ondo karkashin jam'iyyar adawa ta PDP a jihar.

A gobe Alhamis ne PDP ta ayyana za ta gudanar da zaben fidda gwani, kuma akalla akwai masu neman tikitin jam'iyyar guda 3 da hankali ya fi karkata a kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel