“Abin da Ke Hana Turawa Suka Dena Shigowa Yin Kasuwanci a Najeriya”, CNPP Ta Gargadi Tinubu

“Abin da Ke Hana Turawa Suka Dena Shigowa Yin Kasuwanci a Najeriya”, CNPP Ta Gargadi Tinubu

  • An yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya kawo karshen matsalolin tsaro don jawo turawa su zuba hannun jari a kasuwannin Najeriya
  • Kungiyar jam'iyyun siyasar Najeriya (CNPP) ta yi wannan kiran inda ta gargadi gwamnatin Tinubu akan kashe-kashen fararen hula
  • Kungiyar ta ce tattalin arzikin Najeriya zai kara tabarbarewa idan har ba a samu yawaitar turawan da ke shigowa yin kasuwanci a kasar ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kungiyar jam'iyyun siyasar Najeriya (CNPP), ta nemi gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali wajen magance rashin saka hannun jarin turawa a kasuwancin Najeriya.

CNPP ta fadi dalilin turawa na janye jiki daga Najeriya
Kungiyar CNPP ta nemi Tinubu ya kawo karshen matsalar tsaro don jawo saka hannun jarin turawa a Najeriya. Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

Abin da za faru da tattalin arzikin Najeriya nan gaba - CNPP

A cewar kungiyar, tattalin arzikin Najeriya zai kara tabarbarewa idan har turawa suka ci gaba da janye jiki daga yin kasuwanci a kasar, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya fadi babban burin Tinubu kan talakawan Najeriya, ya roki 'yan kasar kan hakuri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan martani ne da CNPP ta yi ga jawabin shugaban kasa Bola Tinubu na murnar shiga sabuwar shekara, inda ta ce:

"Gwamnatin Tinubu na tutuniyar nemo masu zuba hannun jari daga kasashen waje, amma hakan ba zai yiyu ba saboda matsalolin tsaro da suka addabi kasar."

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakin sakataren watsa labarai na kungiyar, Kwamred James Ezema a cewar rahoton Daily Post.

CNPP ta nemi a kawo karshen matsalolin tsaro a Najeriya

A cewar sanarwar:

"Kullum Tinubu na cewa kasashen waje kofar Najeriya a bude take don yin kasuwanci, amma wa zai zo kasar da matsalar tsaro ta yi wa katutu?
"Yawan suturu kawai gwamnatin Tinubu ta iya, amma babu aiki a kasa, zuwa yanzu ya kamata gwamnatin ta fara cika alkawurran da ta dauka lokacin zabe."

Kara karanta wannan

Harin Filato: Peter Obi da wasu yan siyasa da suka ziyarci wadanda abin ya shafa, sun ba da kudi

Kungiyar ta kuma gargadi shugaban kasar kan kashe-kashen farar hula da ake yi a fadin kasar, tana mai cewa hakan babbar illa ce ga yadda kasashen duniya ke kallon Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Har sai an samar da tsaro kuma gwamnati ta tabbatar da bin doka sannan turawa za su shigo Najeriya su yi kasuwanci."

Tinubu zai kashe naira biliyan 100 don dawo da shirin ciyar da dalibai abinci

A wani labarin, gwamnatin shugaba Tinubu ta ce za ta kashe akalla naira biliyan 100 don dawo da shirin ciyar da dalibai abinci, da nufin rage yawan yarasa marasa zuwa makaranta.

Shugaba Tinubu yayin rattaba hannu kan kasafin kudin 2024, ya ce hakan ne kawai zai taimaka wajen bunkasa harkar koyo da koyarwa a matakin farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel