Litar Fetur Ta Haura N900 Yayin da Karancin Mai Ya Kara Ta'azzara a Jihar Sakkwato

Litar Fetur Ta Haura N900 Yayin da Karancin Mai Ya Kara Ta'azzara a Jihar Sakkwato

  • Abubuwan sun ƙara dagulewa yayin da aka fara dogon layi a wurin ƴan bunburutu domin sayen mai a jihar Sakkwato
  • An tattaro cewa mafi akasarin gidajen mai ba su buɗe ba yayin da ƴan kadan da suka fito aiki suna sayar da lita N900 zuwa N1000
  • Kakakin IPMAN na jihar Sakkwato ya ce babu mai a mafi yawan manyan wuraren aje mai da ke faɗin ƙasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - An wayi gari da dogayen layuka a wurin 'yan bunburutu a sassan jihar Sokoto yayin da karancin man fetur ke kara ta'azzara.

Wakilin jaridar Daily Trust ya zagaya wasu wurare a kwaryar birnin Sakkwato kuma ya ga galibin gidajen mai sun rufe sai ƴan kalilan.

Kara karanta wannan

Kaduna: Farashin litar fetur ya haura N1,000 yayin da aka fara dogon layi a gidajen mai

Dogon layi a gidan mai.
Karancin man fetur ya kara tsananta a sassan jihar Sokoto Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Gidajen man da suka fito suna aiki sun kara tsadar litar fetur zuwa tsakanin N900 da N1000 yayin da ƴan bunburutu ke sayar da galan mai cin lita 5 kan N6,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Na sayi rabin galan kan Naira 3000 a wurin ƴan bunburutu bayan bin dogon layi. Ban san ina kasar nan ta dosa ba, wannan gwamnatin ba ta damu da talakawa ba," in ji wani ɗan acaɓa.

Wani ɗan acaɓa na daban mai suna Zayyanu Shehu ya ce ya sayi lita biyar na man fetur a kan Naira 6000.

Ya ƙara da cewa a wasu wuraren ma galan ɗin fetur ya kai N7000 amma shi ya saya a kan N6000, rahoton Leadership.

Wani ɗan Napep, Abdullahi ya ce bisa tilas ya tashi daga aiki tun da yamma saboda ba zai iya bin dogon layi kuma ya sayi mai a N1000 kowace lita ba.

Kara karanta wannan

Masu kantin da ya hana 'yan Najeriya sayayya sun amsa gayyatar hukumar FCCPC

Me ya kawo ƙarancin fetur?

Kakakin ƙungiyar ƴan kasuwar man fetur (IPMAN) reshen jihar Sakkwato, Alhaji Nasiru Aliyu Gidan Kanawa, ya danganta halin da ake ciki da rashin mai a Depot.

"Babu mai a Warri, Patakwal da Legas, muna da mambobin da suka tura kudin motoci 10 amma ko ɗaya ba su samu ba.
"Ba za ku samu mai a ma'ajiyar man fetur mallakar manyan ƴan kasuwa kamar AA Rano, Danmarian, Matrix da Zamson ba. Duk abin da kuke ji daga NNPCL karya ne,” inji shi.

Karancin man fetur ya ta'azzara

A wani rahoton kun ji cewa an wayi garin Alhamis da ganin dogayen layin mai a wasu jihohin kasar nan ciki har da Kano, Gombe, Anambra da babban birnin tarayya Abuja.

Rashin samun man ya kara ta'azzara farashin ababen hawa yayin da wasu gidajen man su ka ku budewa ballantana su sayarwa masu bukata man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel