Ango dake aiki kan na'ura mai kwakwalwa yayin bikinsa ya janyo cece-kuce

Ango dake aiki kan na'ura mai kwakwalwa yayin bikinsa ya janyo cece-kuce

  • Bayyanar wani bidiyon ango yana latsa na’urarsa mai kwakwalwa a ranar bikinsa ya janyo cece-kuce
  • A bidiyon anga amaryarsa tana dariya a lokacin da angon nata yake latsa na’urar cike da annashuwa
  • Mutane da dama sunyita tsokaci suna cewa ga dukkan alamu ayyukansa yakeyi a ranar daurin aurensa

India - Wani bidiyo wanda yayi ta yawo a kafar sada zumunta ta Instagram na ango yana latsa na’urar mai kwakwalwa wurin shagalin bikinsa ya janyo cece-kuce.

Bidiyon wanda mutane da dama suka yi ta cewa ga dukkan alamu yana yin ayyukansa ne duk da kasancewar ranar daurin aurensa ne.

KU KARANTA: Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna

Ango dake aiki kan an'ura mai kwakwalwa yayin bikinsa ya janyo cece-kuce
Ango dake aiki kan an'ura mai kwakwalwa yayin bikinsa ya janyo cece-kuce. Hoto daga @dulhaniyaa
Asali: Instagram

Yayin da yake tsaka da latsa na’urar an hango bakinsa suna jiransa don ya kammala aikin a fara shagulgulan bikin.

An hango amaryar a tana dariya a lokacin da ta hango angon nata yana aiki. Take a nan jama’a suka fara tsokaci iri-iri kowa yana tofa albarkacin bakinsa. Yayin da wasu suke cewa yana aiki ne a na’urar wasu kuma sun ce yana gwadawa dayan mutumin wani abu ne a cikin na’urar.

Kara karanta wannan

Ku Yi Murabus Daga Mukamanku Ko Na Sallameku, Gwamna Ya Gargadi Makusantansa

Jama'a sun yi martani

Wani babunathraja yace:

Bana tunanin aiki yakeyi kawai yanaso ya bude na’urar ne.

Savi_shetty_8 tace:

Da alamu ya mayar da hankalinsa sosai akan aikin... yana aiki tukuru a kowanne hali ya tsinci kansa.

Joghosh kuma yace:

Muna da yanke hukunci daga ganin abu ba tare da bincike ba. Ko wanne kamfani ai suna daga kafa idan irin wannan babbar ranar tazowa mutum.

Wani alpha_omega_001 ya rubuta:

Aure babban lamari ne saboda sau daya yake faruwa a rayuwa.. kodai ka mayar da hankali akan aiki ko kuma akan rana daya a kore ka daga aiki.”

KU KARANTA: Matar tsohon minista ta kwanta dama tana da shekaru 91 a duniya

Muna kokarin ceto Sarkin Jaba, El-Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna tace tana aiki tare da gwamnatin jihar Nasarawa da kuma jami'an tsaro daga jihohin biyu wurin ceto sarkin Jaba, Gyet Muade wanda miyagun 'yan bindiga suka sace a ranar Litinin, Channels TV ta wallafa.

Kara karanta wannan

Ikedi Ohakim: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Imo

Miyagun 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace basaraken mai shekaru tamanin da uku a duniya yayin da yake gonarsa dake yankin Gitata na jihar Nasarawa wanda ke da iyaka da Jaba a jihar Kaduna.

Kamar yadda ChannelsTV ta ruwaito, a yayin jawabi ga wasu jami'an gwamnati da hukumomin tsaro a fadarsa dake masarautar Jaba, Gwamna El-Rufai ya samu wakilcin kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel