Lizzy Anjorin Ta Bar Musulunci, Ta Koka Kan Yadda Babu Wanda Ya Kare Ta Lokacin Da Ake Tsangwamarta

Lizzy Anjorin Ta Bar Musulunci, Ta Koka Kan Yadda Babu Wanda Ya Kare Ta Lokacin Da Ake Tsangwamarta

  • Shahararriyar ‘yan wasan kwaikwayo na Yarbawa, Lizzy Anjorin ta gargadi mutane da su guji hada ta alakanta ta da Musulunci ko sunan Musulmai
  • ‘Yar wasan kwaikwayon ta ce ta fi son a kirata da sunanta na gargajiya madadin alakanta ta da addinin da ba su taimake ta ba a baya
  • Lizzy ta ce lokacin da ake yakarta a kafafen sadarwa babu wani Musulmi ko wata kungiya ta Musulmai da su ke goyi bayanta ko taya ta fada

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas - Shahararriyar ‘yan wasan kwaikwayon ‘Nollywood’, Lizzy Anjorin ta gargadi masu kiranta da sunanta na Musulunci.

Anjorin ta bayyana haka ne a wani faifan bidiyon Instagram inda ta ce ta fi son a kira ta da sunanta na gargajiya, Yeye Mesho, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

NYSC: Hannatu Musawa Ta Sake Sabon Martani Game Da Bautar Kasa, Ta Gargadi Mutane

Lizzy Anjorin ta ce daga yau ta bar Musulunci tun da babu wanda ya kare ta lokacin matsi
Lizzy Anjorin Ta Bayyana Cewa Ta Bar Musulunci Tun Da Babu Wanda Ya Tsaya Mata A Baya. Hoto: @lizzyanjorin_original.
Asali: Instagram

Meye Anjorin ta ce kan Musulmai?

Ta ce a yanzu ba ta da wata alaka da Musulmai ko Musulunci saboda lokacin da ake cin zarafinta a kafar sadarwa kan shiga Musulunci babu wani Musulmi ko wata kungiya da ta kare ta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ku kalli bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun soki Anjorin kan kalamanta inda su ke cewa daman babu abin da ta iya kullum sai fada da jama’a.

Martanin mutane da dama kan bidiyon Anjorin.

crowny_wealth:

“Akwai bambanci tsakanin mai surutu da mai magana don kansa da kuma komawa mahaukaciya a hankali, ta yaya za a ce mutum daya na fada da kowa.”

kemilizzy23:

“Saboda kin zabi kina fada shi yasa, kowa kin yi fada da shi yanzu kin gaji.”

nickipresh:

“Daga Kiristanci zuwa Musulunci, daga Musulunci zuwa Yeye.”

Kara karanta wannan

Jan aiki: Sojojin Najeriya sun lalata wata matatun mai da ake aiki ba bisa ka'ida ba

roslyn_anointed_emmanuel:

“Ya kamata su ba ta taimako, ta na bukatar taimako.”

dr_alwaysrozy:

“Daman tun farko ba Musulmar kirki ba ce.”

ndagiamir:

“Ta yaya mutane za su kare shirme, Allah ya sauwaka miki.”

g_abisola:

“Na fi zargin malaman da su ka ba ki sarautar Borokini Adini, Msheeww.”

i_am_omoladeabimbola:

“Ku na wasa ai, da Kirista ce amma yanzu ta sake barin Musulunci shirme kawai.”

Jaruma Mercy Aigbe Ta Bayyana Darussan Da Ta Koya A Aikin Hajji

A wani labarin, 'yar wasan kwaikwayo na 'Nollywood', Mercy Aigbe ta bayyana irin darussan da ta koya yayin ziyarar aikin hajji a Saudiyya.

Aigbe ta ce abin mamaki a Musulunci babu bambanci tsakanin mai kudi ko talaka, babba da yaro ko kuma fari da baki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel