Mijina Ya Daina So Na, Kuma Yana Mun Barazana da Rayuwa, Mata Ta Nemi Saki a Kotu

Mijina Ya Daina So Na, Kuma Yana Mun Barazana da Rayuwa, Mata Ta Nemi Saki a Kotu

  • Matar aure ta kai ƙarar mijinta gaban Kotu, ta nemi a raba auren saboda ya daina nuna mata soyayya kuma yana mata barazana
  • Mijin mai suna Aminu ya faɗa wa Alkali cewa bai shirya rabuwa da matarsa ba, yana rokon a ba shi lokaci ya rarrashe ta
  • Daga karshe Alkalin ya sake ɗage karar domin bai wa Magidancin damar neman sulhu da mai ɗakinsa

Kwara - Wata matar aure, Misis Amudalat Taiye, ta garzaya gaban Kotun yanki mai zama a cibiyar Igbora, Ilorin, babban birnin jihar Kwara, inda ta roki Alkali ya raba aurenta da Abdulwaheed Aminu.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa matar ta nemi Kotu ra datse igiyoyin aureta da mahaifin yaranta uku kuma a bata dama ta ci gaba da kula da 'ya'yan.

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: An Shawarci Tinubu Da Kar Ya Yi Kuskuren Nada Kai Da Buhari Ya Yi A Lokacinsa

Matsalolin ma'aurata a Kotu.
Mijina Ya Daina So Na, Kuma Yana Mun Barazana da Rayuwa, Mata Ta Nemi Saki a Kotu Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Amudalat ta bayyana cewa a halin yanzu zaman hakuri take da mai gidanta, baya ƙaunarta kuma yana mata barazana, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Haka zalika mai shigar da ƙara ta buƙaci Kotu ta tilastawa Aminu ya riƙa biyan N30,000 kowane wata domin kula da yaransu uku da suka haifa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin Mijin ya amince da buƙatar mai ɗakinsa?

Wanda ake ƙara, Abdulwaheed Aminu, ya faɗa wa Kotu cewa ba shi niyyar sakin matarsa kuma ya roƙi Alkali ya ba shi wata biyu domin manya su shiga ciki a samu sulhu.

Sai dai matar ta kafe kan bakarta ta raba auren, inda ta ƙara da cewa ba ta buƙatar sulhu domin a ganinta Aminu ba zai taɓa canja mugayen halayensa ba.

Wane mataki Alkali ya ɗauka?

Alkalin Kotun, mai shari'a AbdulQadir Umar, ya shaida wa matar cewa doka ta ba da damar yin sulhu, musamman idan ɓangare ɗaya ya nuna a shirye yake ya sauya don a samu zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Rashin Daraja: Magidanci Ya Maka Surikansa Kara a Gaban Kotun Shari'ar Musulunci a Jihar Kano Kan Abu 1 Rak

Umar ya kara da cewa mai yuwuwa rashin halartar zaman Kotu da mijin ya yi yana da alaƙa da kokarin neman a samu sulhu da zaman lafiya a zaman auren.

Bisa haka ya ƙara ɗage zaman sauraron ƙarar zuwa ranar 25 ga watan Yuli, 2023.

"Yana Kaunata Duk da Bani da Hali" Wata Mata Ta Saki Hotunan Mijinta

A wani labarin na daban kuma Wata zankadediyar mata ta hadda kace-nace bayan ta wallafa Hotunan jibgegen mijinta tare da kalaman soyayya.

Yayin da ta saki Hotunansu tare, kyakkyawar matar ta ce Mijinta na tsananin kaunarta duk da tana da halaye mara kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262