Matashiyar Budurwa Ta Fice Daga Makaranta, Ta Samu N2.1bn a Cikin Wata Shida

Matashiyar Budurwa Ta Fice Daga Makaranta, Ta Samu N2.1bn a Cikin Wata Shida

  • Wata budurwa mai shekara 21 wacce ta bar makaranta ta samu N2.1bn a cikin wata shida ta hanyar bayar da hayar gidaje a Airbnb da koyawa wasu harkar
  • Ta bayyana cewa ta koya ne daga wajen tsohon ubangidanta inda ta cimma burinta da ƙara wa kanta ilmi a yanar gizo
  • Ta yi iƙirarin cewa tana da izni daga wajen masu gidajen, tana biyan haraji sannan tana bin doka yadda ya dace

Inayah McMillan tana da burin yin rayuwa irinta fantamawa. Ta bar makaranta bayan shekara ɗaya da shigarta inda ta fara neman hanyoyin da za ta riƙa samun kuɗaɗe a yanar gizo.

Ta jaraba kasuwancin yanar gizo, yin odar kaya da zuba jari, amma babu wanda ta samu nasara a cikinsa.

Matashiyar budurwa ta samu N2bn cikin wata shida
Budurwar tace ta samu kudin ne ta hanyar bayar da haya Hoto: NYpost.com
Asali: UGC

Bayar da haya

Daga nan sai ta gano bayar da haya, inda ta ke hayar gidaje daga nan ta kuma bayar da hayarsu ga waɗanda za su yi amfani da su na wani ɗan lokaci a shafuka irinsu Airbnb, cewar rahoton New York Post.

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Nemi Kotu Ta Gintse Aurenta Na Shekaru 14 Da Mijinta, Ta Bayar Da Dalili

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta bayar da hayar gidaje 11 a St. Louis inda ta mayar da su abin samun riba sosai, a cikin wata ɗaya kawai ta samu kuɗi sun kai $60,000.

Ba ta dakata anan ba

Ta fara bayar da horo kan horaswa a kan kasuwanci tare da saurayinta Bryson, domin koyawa wasu yadda za su yi irin abinda ta ke yi.

Ta yi iƙirarin cewa sun samu miliyan ɗinsu ɗaya ta farko a watan Oktoban 2022 sannan suka ƙara samun wata miliyan biyu zuwa ƙarshen shekarar.

Ta bayyana labarinta ne a wani bidiyon YouTube mai "Yadda na samu $3m a cikin wata shida a matsayin ƴar kasuwa mai shekara 20), wanda sama da mutum 1.2m suka kalla ya zuwa watan Yunin 2023.

A cikin bidiyon, ta ɗora nasararta akan zuciya mai kyau da ta ke da ita, zunmar aiki da karantar da kanta.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wata Mata Manajar Banki, Sun Dade Suna Yi Mata Gargadi

Ta bayyana cewa bata fito ba daga gidan attajirai, amma ta samu darasin yin hakan ne daga wajen tsohon ubangidanta, wanda hamshaƙin attajiri ne bayan ya ɗauketa a matsayin mai raino bayan ta bar makaranta.

Budurwa Mai Samun N3.7m a Wata Ta Bayyana Irin Mijin Da Ta Ke So

A wani labarin kuma, wata budurwa mai samun albashi mai tsoka ta bayyana irin mijin da ta ke so ta samu a matsayin abokin rayuwarta.

Budurwar mai samun N3.7m a wata tace dole sai wanda yake son ya aureta yana samun abinda bai yi ƙasa da N3m a wata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel