Ni Kaɗai Za Ku Haifa: Yarinya Ta Shiga Ruɗani Bayan Ganin Mahaifiyarta Da Ciki

Ni Kaɗai Za Ku Haifa: Yarinya Ta Shiga Ruɗani Bayan Ganin Mahaifiyarta Da Ciki

  • Wata yarinya ta shiga tashin hankali da bakin ciki lokacin da ta gano mahaifiyarta na dauke da juna biyu
  • Yarinyar ta ce ita kam bata son ta samu kanne maza ko mata saboda irin soyayyar da iyayenta suke mata
  • Mahaifiyar ta yi iya bakin kokarinta don ganin ta kwantar mata da hankali amma yarinyar ta yi kunnen uwar shegu

Wata karamar yarinya ta shiga cikin bakin ciki da rudani bayan ta gano mahaifiyarta na dauke da juna biyu.

Yarinyar ta kasance ita kadai ce a wurin iyayenta na tsawon lokaci, kuma tana jin dadin hakan kasancewarta ita kadai.

yarinya
Yarinyar lokacin da take magana, Hoto: @littleviv1
Asali: TikTok

A cikin wani faifan bidiyo a TikTok, ta ce tana jin dadin kasancewa ita kadai saboda mahaifan nata suna ba ta kulawa ta musamman, kuma bata son a rinka hada ta da wani sabon jariri ko jaririya a gidan wurin bata kulawan.

Kara karanta wannan

Ya Cika Mako: Budurwa Ta Ba da Labarin Yadda Ta Kare Bayan Ziyartar Saurayinta

Mahaifiyarta ta yi iya bakin kokarinta don ganin ta sauya tunaninta

Mahaifiyarta ta yi kokarin tabbatar mata da cewa samun karin haihuwa ba zai hana komai daga irin kulawa da soyayyar da suke mata ba, ta ce za su so ta sosai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama da suka kalli faifan bidiyon sun yi mamakin karamar yarinya kamar wannan za ta iya neman ta kasance ‘ya daya tilo.

Legit ta tattaro wasu daga cikin martanin da mutane suka yi

@EKSUkayamata:

“Bata son suna hada jin dadi da kannenta wurin holewa da jin dadin rayuwarsu.”

@OdowguGaga:

“Jaririn ya kai a haifeshi, don Allah karku saurare ta, hhh.”

@Citybabe2512:

“Wasa kike yi ne.”

@mldecollectlon7:

“Wannan yarinyar mayya ce.”

@Ifèomàd:

“Wannar iri na ce lokacin da nake karama in mahaifiyata tana da ciki addu’a nake kar ta haifi ‘ya mace.”

Kara karanta wannan

Na Tuba: Budurwar Da Ke Tallan Kanta Da Hotunan Batsa Ta Tuba, Ta Mika Rayuwarta Ga Addini

@Nedu3030:

“Nima haka nake, in naji mahaifiyata na da ciki zan ji bakin ciki, zama kai kadai a wurin iyaye yafi dadi akan yawan kanne.”

@PatyIsah:

“A zane ta mana, ita kadai za a haifa ne?”

@arayodeadedolapo:

“Don Allah in kuna son haihuwa ku yi da wuri, da na dan shekara 16 yana son kashe kansa tun da aka ce masa mahaifiyarka ta haihu.”

Budurwa Ta Bada Shawarar Yadda Za a Yi Aure Da Kudi N400,000 Kacal

A wani labarin, wata matashiya 'yar Najeriya ta bai wa masoya masu son aure shawaran yadda za suyi aure da kudi kalilan ba tare da wata karya ba.

Budurwar mai suna @ButterBibi ta ce masoyan za su iya samun dakin taro ko da a majami'a ne su rangada aurensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel