Na Gaji: Mahaifiya Ta Ɗaure Ƙafar Ɗanta a Kujera Saboda Ɓarnar Da Yake Yi Mata a Shago

Na Gaji: Mahaifiya Ta Ɗaure Ƙafar Ɗanta a Kujera Saboda Ɓarnar Da Yake Yi Mata a Shago

  • Wata mata ta daure kafar danta karami a jikin kujerar shagonta saboda irin barnar da yaron ke yi mata
  • A wani faifan bidiyon da aka yada a TikTok an gano matar ta daure kafar yaron da zani yadda ba zai motsaba da yawa ba
  • Ta ce irin barnar da yake yi ne yasa ta daureshi, ta nuna yadda yaron ya yi kaca kaca da shagon nata

An wallafa wani faifan bidiyo a TikTok da ya jawo cece-kuce, inda aka gano wata mata ta daure kafar danta karami a jikin kujera saboda damunta da yake yawan yi.

A cikin faifan bidiyon wanda wani matashi mai suna @raymist ya yada, an gano matar cikin fushi tana nuna yadda yaron ya yi kaca-kaca da shagon.

karamar yarinya
Yaron da aka daure, Hoto: @raymist
Asali: TikTok

Daga bisani sai ta daure kafarshi da zani ta hada da kafar kujerar da ke cikin shagon don hana shi motsi da yawan yawo.

Kara karanta wannan

Hayan Gidan N2m a Shekara a Legas: Babu Ruwa, Ga Tsadar Wutan Lantarki

Jama'a sun yi ta cece-kuce, inda suka tofa albarkacin bakinsu game da abin da matar ta yi. Ga kadan daga ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu

@ayomide.o21:

“Zan iya tuna lokacin da aka yi wa dan autanmu haka wanda ba ya jin magana, kai Allah ya saka wa iyayenmu.”

@seunay2:

“Yana da kyau, amma nan gaba a daura kafarshi a jikin wani abu da zai iya janshi.”

@simplyarike5:

“Mahaifiyata kullum ta na fada min yadda take daure kafata a jikin keken dinki.”

@naeem_147:

“Kar ki kuskura ki gwada haka a kasashen waje, za su kwaceshi daga gare ki, ke kuma a kaiki gidan gyaran hali.”

@iremidetemmy0:

“Inda mutane sun san irin faman da nake da nawa dan, abin da wannan yaron ya yi ba komai bane.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Uba Goye Da Dansa Da Tsakar Dare Ya Yadu, Ya Ce Baya Barinsa Ya Yi Bacci

@micochi4real:

“A bi ma wannan yaron kadunsa, za a sanar da wurin haduwa nan kusa.”

Yadda Zaku yi Aure Akan N400,000 Kacal, Budurwa Ta Bai Wa Masoya Shawara

Wata budurwa ta bai wa masoya masu hankoron yin aure cikin sauki shawaran yadda zasu yi aure ba tare da karya ba akan kudin da bai wuce N400,000 kacal.

Ta ce ma'auratan in sun cire karya, za su yi aurensu ba tare da wata matsala ba, inda ta ce zasu iya zuwa ko cikin majami'a su yi amfani da dakin taronsu, daukan hoto kuma ta ce zasu iya nemo aron wayar hannu ko da iPhone ce suyi amfani da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel