Wata Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Bayan Ta Gano Sunan Sa Na Ainihi

Wata Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Bayan Ta Gano Sunan Sa Na Ainihi

  • Wani matashi ɗan Najeriya ya bayyana yadda wata ƙawar sa ta rabu da saurayin ta bayan sun kwashe wata bakwai suna soyayya
  • Matashin ya sanya hirar da suka yi da budurwar wacce tayi ƙorafin cewa ta gano ainihin sunan saurayin ta shine Bashiru
  • Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su wannan abin da tayi inda wasu ke ganin dama can dai ta ƙosa su rabu ne

Wata budurwa ƴar Najeriya ta kawo ƙarshen soyayyar da suke yi da saurayin ta bayan ta gano sunan sa na gaskiya.

Budurwar ta gano cewa saurayin ya sharara mata ƙarya wajen sunan sa, inda ainihin sunan sa shine Bashiru a maimakon Bash da yace mata.

Budurwa
Wata Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Bayan Ta Gano Sunan Sa Na Ainihi Hoto: Twitter/Deevybs
Asali: UGC

Wani matashi mai amfani da sunan Deevybs, a Twitter, shine ya sanya hirar da suka yi da budurwar inda take ta ƙorafi akan lamarin.

Kara karanta wannan

Shirin Ya Kwance: Amarya Ta Karye Ana Saura Kwana Kaɗan Biki, Ta Je Wajen Biki a Keken Guragu

Budurwar ta koka kan cewa dole ta rabu da shi domin bata san yadda zata tunkari ƙawayenta ta gaya musu cewa sunan saurayin na gaskiya Bashiru ne ba Bash ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Budurwar ta nuna cewa Bashiru yayi ƙauyanci da yawa yayin da Bash yayi kama da sunan irin mutanen ƙasar Turkiyya.

Rubutun nasa na cewa:

"Wata ƙawata ta rabu da saurayin ta wanda suke soyayya na tsawon wata bakwai, bayan ta gano sunan shi na gaskiya shine Bashiru ba Bash ba. Mata suna da abin ban mamaki."

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kan wannan matakin da budurwar ta ɗauka.

Ga kaɗan daga ciki:

@B2kMrwhyte ya rubuta:

"Bash. da Bashiru ban ga wani bambanci a ciki ba."

@_lexzy ya rubuta:

"Ta yaya zan gayawa budurwa ta cewa cikakken suna na shine Akpojuvetus ba juve ba."

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Mai Kula Da Fasinjojin Jirgin Sama Ta Ɗauki Juna Biyu Ba Ta Sani Ba, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

@ OlufunkeRachel ta rubuta:

"Ina da aboki mai suna Bash, yanzu ya tabbatar min da cewa shima sunan shi Bashiru."

@ornamentisback ya rubuta:

"Ba wani abu bane mai wahala, zata iya kiran shi da Bash ko Bashir, sannan idan ƙawayen ta sun tambayeta sai tace musu Bash shine Bashir a taƙaice. Ban ga wani dalilin da zai sanya sai tayi wani bayani ga kowa ba.
"Kawai dai tana neman abinda zata fake da shine su rabu."

@ godson_merit ya rubuta:

"Ƴar'uwata tayi irin hakan. Ya gaya mata cewa sunan shi Theo ita duk ta ɗauka Theodore ne bata san cewa sunan shi THEOPHILUS ba."

Ana Saura Sati Ɗaya Biki, Amarya Ta Karye Ta Ɓishe Da Zuwa Waajen Bikin a Keken Guragu

A wani labarin na daban kuma, wata amarya ta samu koma baya ana dab da a ɗaura mata aure.

Sai dai duk da wannan koma baya taje wajen bikin ta amma fa a wani yanayi na daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel