Matashiyar Sojan Najeriya Ta Koka Kan Rashin Saurayi, Tace Samari Tsoronta Suke Yi

Matashiyar Sojan Najeriya Ta Koka Kan Rashin Saurayi, Tace Samari Tsoronta Suke Yi

  • Wata matashiyar sojan ruwa ƴar Najeriya ta koka kan rashin samun mashinshini da take fama da shi
  • Kyakkyawar budurwar ta bayyana dalilin da ya sanya samari da dama ba su iya tunkarar ta da batun soyayya
  • Bidiyon matashiyar ya ɗauki hankula sosai inda mutane da dama suka yi ta sharhi akan sa

Wata matashiyar budurwa ƴar Najeriya, mai amfani da sunan @naval_goddess a TikTok, wacce ke aiki da rundunar sojojin ruwan Najeriya, tayi wani bidiyo da ya ɗauki hankulan mutane.

Matashiyar budurwar ta ɗora wani ɗan gajeran bidiyo a TikTok inda ta nuna yadda samari ke tsoron ta saboda khakin ta na soja.

Budurwar soja
Matashiyar Sojan Najeriya Ta Koka Kan Rashin Saurayi, Tace Samari Tsoronta Suke Yi Hoto: TikTok/naval_goddess
Asali: UGC

Ta bayyana cewa duk da tana da matuƙar son ganin ta samu saurayi, hakan yayi mata wahala saboda yanayin aikin ta.

Nan da nan samari da dama suka yi ta yin tururuwa a ƙasan wajen yin sharhi kan bidiyon, suna ƙoƙarin jaraba sa'ar su.

Kara karanta wannan

Ango Yayi Abin Mamaki, Ya Nuna Wani Halin Kirki Da Ya Taɓa Zuciyoyi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu kaɗan daga cikin su sun so sanin cewa ko tana da zuciya mai kyau wacce zata yi maraba da soyayyar su.

Bidiyon ya yaɗu sosai

Bidiyon ya yaɗu sosai inda sama da mutum dubu shida suka yi sharhi akan sa, sannan sama da mutum dubu arba'in da takwas suka danna masa alamar so.

Ga kaɗan daga cikin ra'ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Legit Hausa ta tattaro:

user59511241824223 ya rubuta:

"Kin cika abin ban dariya sosai."

Prince James Adex ya rubuta:

"Shin ko zan iya samun wannan kyakkyawar."

KELVYN BOY BA QUAME SWEET ya rubuta:

"Ina neman iznin a bani dama na jaraba sa'a ta."

Sthesh ya rubuta:

"Ki zama jagora na zama ɗan aiken ki."

Pnprove ya rubuta:

"Taa duk wanda baya jin tsoron komai a ƙasar nan sai ya ƙara sanya mana tsoro."

Kara karanta wannan

Mutuwa Rigar Kowa: Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Yanke Jiki, Ta Rasu a Layin Zabe a Zamfara

Collen Conny ya rubuta:

"A wajena kina da mafaka, ki zo kawai mu ji daɗin ƙauna."

Ango Yayi Abin a Yaba, Ya Ziyarci Abokinsa a Gadon Asibiti Wanda Bai Samu Zuwa Bikin Sa Ba

A wani labarin na daban kuma, wani ango ya garzaya asibiti ana ɗaura masa aure domin duba abokin sa wanda baya da lafiya.

Abokin nasa dai rashin lafiya ce ta kama shi bayan yayi shirin zuwa wajen bikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel