Ango Yayi Abin a Yaba, Ya Ziyarci Abokinsa a Gadon Asibiti Wanda Bai Samu Zuwa Bikin Sa Ba

Ango Yayi Abin a Yaba, Ya Ziyarci Abokinsa a Gadon Asibiti Wanda Bai Samu Zuwa Bikin Sa Ba

  • Bidiyon wani ango da ya nuna wani na hali na kamala ya ɗauki hankulan mutane sosai a yanar gizo
  • Angon ana ɗaura masa aure ya garzaya asibiti domin duba abokin sa wanda rashin lafiya ta hana ya samu zuwa wajen ɗaurin auren
  • Mutane da dama sun yaba da wannan halayyar da angon ya nuna inda suka yi ta masa ruwan addu'o'i

Wani bidiyo wanda ya sosa zuciyoyi ya nuna lokacin da wani ango ya ziyarci abokin sa wanda bai samu zuwa ɗaurin auren sa ba, saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.

A cikin bidiyon, angon yayi bayanin cewa, abokin nasa ya faɗa rashi lafiya bayan ya gama shirin bikin wanda hakan ya sanya bai samu zuwa ba.

Angon
Ango Yayi Abin a Yaɓa, Ya Ziyarci Abokinsa a Gadon Asibiti Wanda Bai Samu Zuwa Bikin Sa Ba Hoto: TikTok/@deep_mind_24
Asali: TikTok

Ana ɗaura musu aure shi da amaryar sa, sai angon da tawagar abokan sa suka zarce zuwa asibitin domin duba lafiyar sa.

Kara karanta wannan

Mutuwa Rigar Kowa: Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Yanke Jiki, Ta Rasu a Layin Zabe a Zamfara

A asibitin sun haɗu da mara lafiyan wanda ba a ɗaɗe da sallamo shi daga wajen marasa lafiyan da ciwon su yayi zafi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yana kwance akan gadon asibitin inda yake jinya lokacin da angon da abokan sa suka shigo domin nuna masa ƙauna.

Sun taho masa da kayan da abokan ango suka sanya, inda shima ya sanya ƙafin nan suka cigaba da ɗaukar hotuna.

Bidiyon ya sosa zuciya sosai

Wannan halin kirkin da angon da abokan sa suka nuna ya ɗauki hankulan mutane sosai a TikTok, inda suka yi ta yaba musu kan hakan.

Ga kaɗan daga ciki:

@unknown creature ya rubuta:

"Wannan abin ya sosa min zuciya. Allah ya bashi lafiya. Ameen."

@rani_tef ta rubuta:

"Tabbas wannan ibada ce. Allah ya baku zaman lafiya da rayuwa mai albarka."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Kwana 2 Gabanin Zabe, Gwamna Wike Ya Sake Ta da Wa Atiku Hankali

@Journo Mom ta rubuta:

"Wannan ya sanya ni kuka."

@user5797835229475 ya rubuta:

"Allah maɗaukakin sarki ya bashi lafiya."

@Favour Richie ta rubuta:

"Wannan shine abota. Allah yayi muku albarka ku duka."

@Mofti_World ya rubuta:

"Hakan ya sanya ni zubar da hawaye. Mu cigaba da addu'a Allah ya sanya mu samu abokai irin wannan."

@Salma ta rubuta:

"Ya taɓa min zuciya. Allah yayi muku albarka sannan ina masa fatan samun lafiya cikin gaggawa Insha Allah."

A wani labarin na daban kuma, an gwangwaje wata amarya da kyautar miliyoyin kuɗi a ranar bikinta. Bidiyon ya ɗauki hankula sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel