Tsohon Dan Takarar APC Ya Ce Ya Yi Mafarkin Sarauniya Elizabeth II a Aljanna

Tsohon Dan Takarar APC Ya Ce Ya Yi Mafarkin Sarauniya Elizabeth II a Aljanna

  • Adamu Garba ya jawo cece-kuce a Twitter yayin da ya bayyana mafarkinsa na ganin sarauniyar Ingila a aljanna
  • Adamu ya ce sarauniya Elizabeth II jika ce ga Annabi Muhammadu, ya kuma bayyana dalilin fadin haka
  • A bangare guda, mutane da dama sun yi ca a kan rubutunsa, suna ta bayyana ra'ayoyinsu kan wannan babban batu

Najeriya - Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Adamu Garba II ya bayyana wani mafarkin da ya yi na marigayiya sarauniyar Ingila Elizabeth II, inda ya ce ya ganta a aljanna.

Wannan batu na Adamu ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, domin kuwa ya hada da yi mata addu'ar rahama, lamarin da ya ba musulmin Twitter mamaki.

Jama'a da dama sun yi martani, sun bayyana kaduwa da yadda matashin kuma jigon APC, musulmi zai yi addu'o'in rahama ga sarauniyar da ke kan millar addinin kiristanci.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP: An kashe 'yan jiha ta 5000 cikin shekaru 11 a hare-haren 'yan bindiga

Adamu Garba ya ce ya ga sarauniyar Ingila a aljanna
Tsohon Dan Takarar APC Ya Ce Ya Yi Mafarkin Sarauniya Elizabeth II a Ajnanna | Hoto: @adamugarba
Asali: Twitter

Da yake bayyana abin da ya gani a mafarkin, Adamu ya rubuta a shafinsa cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yanzun nan nayi mafarki Queen Elizabeth tana shaqatawa a cikin Jannatul Firdaus. Allah Ya tabbatar da hakan. Ameen!
"Allah shine mai wuta da aljanna, Saboda Haka bana bakin cikin shigan kowa aljanna."

Elizabeth II jinin Annabi ce, inji Adamu

A wasu bidiyo guda biyu da yada a TikTok, kuma ya kawo kan shafinsa na Twitter, Adamu ya ce to ai duk maganar da ake ba dan-adam ke ba da aljanna ko wuta ba.

A bangare guda kuwa, ya ce, sarauniyar jika ce daga cikin jikokin Annabi Muhammadu SAW kuma tana girmama addinin Islama.

Ya ba da misali da yadda gidan sarautar Ingila ta ba da fili aka gina katafaren masallaci a birnin Landan.

Hakazalika, ya ce ya kamata mutane su rage zafin kai, su daina tsarkake kansu a matsayin wadanda ba sa kuskure ko su kadai ne 'yan aljanna.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani bene ya ruguje a wata jihar Arewacin Najeriya

Har yanzu dai ana ci gaba da kai ruwa rana tsakain Adamu da daruruwan mutane a Twitter.

Ga dai abin da yake cewa:

Ina da Dangantaka Mai Karfi da Sarauniyar Ingila Elizabeth II, Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo

A wani labarin, kasar Burtaniya ta ba 'yan Najeriya tabbacin cewa, ba za ta tsoma baki a lamurran zaben 2023 mai zuwa nan kusa ba.

Babbar Kwamishinira Burtaniya a Najeriya, Ms Catriona Laing ce ta bayyana hakan, inda tace Burtaniya za ta tsaya tsaka-tsaki a lokacin zabukan.

Ta bayyana haka ne a Birnin Kebbi ta jihar Kebbi a wata tattaunawa da manema labarai, jaridar Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel