Wata Tsaleliyar Budurwa Yar Kasar Indiya Za Ta Auri Kanta, An Kammala Tsare Biki

Wata Tsaleliyar Budurwa Yar Kasar Indiya Za Ta Auri Kanta, An Kammala Tsare Biki

  • Wata budurwa, Kshamu Bindu, daliba kuma marubuciya yar shekara 24 ta shirya tsaf domin auren kanta a kasar Indiya.
  • Tuni dai an kammala tsara yadda biki zai kasance har ma da garin da za ta tafi hutun masoya wato 'honey moon' ita kadai bayan daurin auren
  • Wannan sabon al'adda inda mutum ke auren kansa da ake kira 'Sologamy' ya fara bazuwa ne a kasashen yamma a baya-bayan nan amma yanzu ya isa Indiya

Indiya - Miss Kshamu Bindu, wata matar yar kasar Indiya tana shirin auren kanta a wani biki na gargajiya da za a yi a ranar 11 ga watan Yunin 2022 a wani wurin bauta da ke birnin Vadodara, a yammacin Gujarat, rahoton Leadership.

Sanye da kayanta na amare, da lalle na zamani wato henna a hannunta da hoda a kanta, amaryar za ta yi zagaye wuta sau bakwai kamar yadda aka saba a auren al'adarsu.

Wata Tsaleliyar Budurwa Yar Kasar Indiya Za Ta Auri Kanta, An Kammala Tsare Biki
Tsaleliyar Budurwa Yar Kasar Indiya Za Ta Auri Kanta, An Kammala Tsare Biki. Hoto: @BBCNews.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za a yi al'adu da aka saba yi kafin aure kamar Haldi (inda ake shafa wa amarya kurkur hade da mai) da sangeet (waka da rawa) a safiyar ranar auren.

Bindu za ta tafi Honey Moon ita kadai bayan daurin aure

Bayan auren za ta tafi hutun masoya wato Honey Moon a Goa inda za ta yi makonni biyu.

Abin da kawai babu a bikin shine ango. Don Miss Bandu tana shirin auren kan ne, wannan shine karo na farko da mace za ta fara auren kanta a Indiya.

"Mutane da dama suna kira na suna fada min cewa ni son kowa ne kin wanda ya rasa," a cewar daliba yar shekaru 24 mai karanta Sociology kuma marabuciya, ta kara da cewa, "Ina fada musu, na yi sa'an auren kai na."

Bayan na auri kai na, zan cigaba da rayuwa ina kaunar kai na da kulawa da kai na a cewar Miss Bindu.

'Sologamy' bikin aure da aka yi inda mutum zai auri kansa, wani lamari ne da ke bazuwa a kasashen yamma cikin yan shekarun nan amma yanzu ya iso Indiya.

Ina Buƙatar Mijin Aure Cikin Gaggawa, In Ji Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya

A wani rahoton, gogaggiyar jarumar fina-fina ta Nollywood a Najeriya wacce aka dade ana damawa da ita, Eucharia Anunobi, ta ce neman mijin aure ta ke yi cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

A wata tattaunawa da BBC Ibo ta yi da ita, ta ce tana neman namijin da zai sanya mata zoben aure a yatsan ta.

Jarumar mai shekaru 56 ta ce tana fatan samun cikakken namiji, wanda ya ke da duk abinda mace ta ke nema a wurin mijin aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel