Ina mugun kaunar matata kamar zan mutu, dan Allah kada ku raba mu, Miji ya roki Kotu

Ina mugun kaunar matata kamar zan mutu, dan Allah kada ku raba mu, Miji ya roki Kotu

  • Wani ɗan kasuwa ta matarsa ta kai shi ƙara Kotu tana neman a raba Auren, ya roki Alkali ka da ya amince da buƙatarta
  • Magidancin ya shaida wa Kotu har yanzun yana masifar kaunar matarsa kuma ba ya son rabuwa da ita
  • Matar dai ta kafa hujjar cewa mijinta na jibgarta har kusan rasa idonta ɗaya ta yi saboda yawan dukanta da yake yi

Abuja - Wani ɗan kasuwa, Monday Francis, ranar Alhamis, ya roki Kotun kostumare dake Jikwoyi, Abuja, kada ta amince da bukatar matarsa mai suna Mercy.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Magidancin ya shaida wa Kotun cewa har yanzun yana matuƙar son matar, ba zai iya rabuwa da ita ba.

Matsalar aure da neman saki a Kotu.
Ina mugun kaunar matata kamar zan mutu, dan Allah kada ku raba mu, Miji ya roki Kotu Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Farancis ya yi wannan rokon ne yayin da yake kare kansa a ƙarar da matarsa Mercy ta shigar da shi gaban Kotu.

Kara karanta wannan

Jaruma mai Kayan Mata ta cigaba da wallafa bidiyoyin Regina Daniels, duk da uwar-watsin da aka yi a kotu

Mijin ya ce:

"Har yanzun ina ƙaunar matata, bana son ta rabu da ni, burinta shi ne ta sake ni ta tsiya. Ta haɗa kai da wasu mutane waɗan da suke ƙara zuga ta a kaina kuma suna faɗa mata ta rabu da ni."
"Ina rokon wannan Kotun mai albarka, Dan Allah ka da ta amince da bukatar matata."

Mai shigar da ƙarar, Mercy, a ɓangarenta ta roki Kotu ta taimaka mata domin ba zata iya cigaba da rayuwa da shi ba.

Ta kuma faɗa wa Kotun cewa Mijinta ya kware wajen jibgarta kuma har kusan rasa idonta ɗaya ta yi sanadiyyar dukan da yake mata.

Wane mataki Kotun ta ɗauka?

Alkalin Kotun, Mai Shari'a Labaran Gusau, yayin da yake yanke hukunci, ya roki ma'auratan su nemi hanyoyin sulhu a waje.

Kara karanta wannan

Ba zan iya cigaba da zama ba, na daina kaunarsa a zuciyata, Mata ta nemi Kotu ta gimtse auren

Daga nan kuma ya ɗage sauraron shari'ar har zuwa ranar 3 ga watan Afrilu, 2022 domin su kawo masa rahoton sasantawar da suka yi.

A wani labarin kuma mun kawo muku Yadda aka gano wata budurwa da aka yi garkuwa da ita tsawon shekara uku ɗauke da ciki wata 8

Yan sanda sun ceto wata dalibar Sakandire mai shirin rubuta WAEC da ta ɓata shekara uku kenan ɗauke da juna biyu.

An kama matashi da mahaifiyarsa da suka haɗa baki suka sace ta, budurwar tace sun bata wasu kwayoyi ya sa ta manta gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel