Jaruma mai Kayan Mata ta cigaba da wallafa bidiyoyin Regina Daniels, duk da uwar-watsin da aka yi a kotu

Jaruma mai Kayan Mata ta cigaba da wallafa bidiyoyin Regina Daniels, duk da uwar-watsin da aka yi a kotu

  • Fitacciyar mai saida maganin matan nan, Jaruma, ta cigaba da ɗora bidiyoyin jaruma Ragina Daniels a shafinta na Instagram
  • Matar da ta daɗe tana jawo cece-kucen ta bayyana taurin kanta a fili duk da shariar da suka yi har aka kaita gidan yari
  • Hakan ya tada ƙura a kafar sada zumuntar zamani, inda Jaruma ta amince yayin da wani mabiyinta yayi tsokaci da cewa, sai ta fitar da kuɗinta

Fitacciyar ƴar Najeriyar wacce tayi suna a kafar sada zumuntar zamanin nan wurin siyar da kayan mata, Hauwa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma, ta ci gaba da wallafa bidiyoyin jarumar Nollywood, Regina Daniels.

Yayin magana da masu amfani da yanar gizo, mai saida kayan matan ta cigaba da ɗora wallafar Regina Daniels a shafinta, duk da irin badaƙalar dake tsakanin su.

Kara karanta wannan

Ina mugun kaunar matata kamar zan mutu, dan Allah kada ku raba mu, Miji ya roki Kotu

Jaruma mai Kayan Mata ta cigaba da wallafa bidiyoyin Regina Daniels, duk da uwar-watsin da aka yi a kotu
Jaruma mai Kayan Mata ta cigaba da wallafa bidiyoyin Regina Daniels, duk da uwar-watsin da aka yi a kotu Hoto daga @jaruma_empire
Asali: Instagram

Jaruma ta wallafa bidiyonta da Regina a asibiti, lokacin da bata da lafiya inda take bata magani.

Mai saida maganin matan ta cigaba da tallata hajarta mai bunkasa jindadi ga maaurata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a nan ta tsaya ba, Jaruma ta kara da amincewa da abunda wani mabiyinta ya lura dashi, na cewa komai zai faru sai ta fanshe kudinta.

Ga wallafar a ƙasa:

Jamaa sun yi martani

Modede_101: "Yanzu idan da ƴan sanda ko kotu zasu ci mutuncinta, wasu mutane za su fara likau da #ayiwajaruma adalci."
Mizspicy_rose: "Har yanzu ana rikicin. Wadannan tsofaffin bidiyo ne, Jaruma na kokarin tabbatarwa duniya cewa Regina tayi amfani da kayayyakinta, sannan ta gyarata."
Triopletschopsandcatering1: "Kwangilar miliyan uku don jawo kasuwa ba karama bace fa."
Chychy_ibe: "Da yanzu za'a sake kama ta, wasu daga cikin ku sai su fara yaɗa cewa an ci zarafinta, amma ta ƙi ƙyale batun "

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

Akorem_: "Ƴar kasuwa mai maida hankali a kan kasuwancinta, tana da lauyoyin da za ta biya."
Iam_ogesandra: "Ta matuƙar bukatar sanin darajar kudinta."

T_nife: "Wannan matar na gadan asibiti a wannan bidiyon, ina tunanin hakan, idan fa tana bata magungunan da basu da dadi ne, meye amfanin tuna wannan lokacin."

Ned Nwoko ya sake sa an cafke Jaruma mai Kayan Mata, alkali ya aike ta gidan yari

A wani labari na daban, fitacciyar mai siyar da kayan mata mai suna Hauwa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma, ta shiga gagarumar matsala da biloniyan dan kasuwa, Ned Nwoko.

Sa'o'i kadan kenan da mai siyar da kayan matan ta gama ciki baki kan yadda ta san mutane da kuma kafar da ta ke da ita saboda yadda aka sake ta bayan Ned ya sa an damke ta.

Kamar yadda rahotanni suka tattaro, an sake kama mai siyar da kayan matan a yanar gizo kuma alkali ya aike ta gidan yarin da ke Suleja.

Kara karanta wannan

Yadda aka gano wata budurwa da aka yi garkuwa da ita tsawon shekara uku ɗauke da ciki wata 8

Asali: Legit.ng

Online view pixel