Adalin miji: Magidanci ya gina gidaje 2 masu kama daya zai aje matansa a ciki

Adalin miji: Magidanci ya gina gidaje 2 masu kama daya zai aje matansa a ciki

  • Wani dan kasar Kenya mai suna Hez Jakamollo ya jijjiga 'yan soshiyal midiya bayan ginawa matansa gidaje guda biyu kyawawa masu kama da juna
  • Kyawawan gidajen suna da tsarin gini iri daya daga rufin har zuwa tagogi, bangon waje da baranda da kayan da ke ciki
  • Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yaba masa bisa daukaka darajar auren mace fiye da daya a wani salo mai ban mamaki

Kenya - Wani dan kasar Kenya ya cika ka'idar auren mace fiye da daya bayan ya gina wa kowacce daga cikin matansa gida domin zaman aure.

Mutumin da aka bayyana sunansa da Hez Jakamollo ya yada hotunan gidajen biyu da ake gab da kammalawa, kuma mutanen Kenya sun yi mamakin yadda gidajen ke kama da juna da kuma kusanci da juna.

Kara karanta wannan

Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB

Adalin miji zai aje matansa a gidaje daban-daban
Adalin miji: Magidanci ya gina gidaje 2 masu kama daya zai aje matansa a ciki | Hoto: Hez Jakamollo
Asali: Facebook

A cikin hotunan da ya yada a shafukan sada zumunta, gidajen da ke da nisan mitoci kadan da juna suna da tsari iri daya, tun daga rufin kwano da tagogi har zuwa bangon waje da baranda.

Ya ce sannu a hankali aikin yana tafiya yadda ya kamata, kuma nan ba da jimawa ba za a kammala shi.

'Yan soshiyal midiya sun jijjiga da ganin jajircewarsa a daidai lokacin da har yanzu auren mace fiye da daya ke ci gaba da jawo cece-kuce a wani bangare na ‘yan kasar Kenya.

Ya rubuta:

"Aiki yana ci gaba, sannu a hankali."

A cikin sashin sharhi, 'yan Kenya da yawa sun yaba masa kan hakan, wasu ma suna ba da ra'ayi kan abubuwan da za a iya karawa a cikin gidajen.

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

Martanin 'yan soshiyal midiya

Ga wasu daga cikin maganganun:

Nancy Anyango Bensouda ta ce:

"Za ku iya "cin abinci" a cikin dare daya, Shagali da yawa, lich! Ina taya ka murna DG.

George Guda ya rubuta

"Na dauki hannu sosai. Ina ga zan shiga cikin wannan da karfin hali. Kyakkyawan aiki jagot!"

Nick Odhiambo ya ce:

"Kuna bukatar gina rami mai zaman kansa na karkashin kasa. Madalla da bamu sha'awa muna taya ka murna!"

Ndede Elizaphan ya ce:

"Hakan yana da kyau. Yanzu, ka kara wata matar."

Tina Tish Aisha Phillips ta rubuta:

"Ina son kusancin dake tsakanin na farko zuwa na biyun. Da dabara sosai. Ina taya ka murna!"

A wani labarin, wasu ma'aurata a garin Kandara da ke Murang'a na kasar Kenya na cikin farin ciki bayan da masu hannu da shuni suka kawo musu dauki bayan shafe shekaru suna rayuwa cikin kunci tare da 'ya'yansu.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka

Peter Waweru, wanda ya kwashe shekaru da yawa baya iya motsawa bayan fama da rashin lafiya, yana zaune ne tare da iyalansa a wani gidan da ke daf da rugujewa.

An yi sa'a, masu mutanen kirki karkashin jagorancin mawakiyar Kikuyu, Anne Lawrence, sun tausaya musu ganin irin mawuyacin halin da suke ciki, inda suka fara fafutukar ginawa Waweru da iyalinsa gida mai mai har ma da bandakinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel