Dama bamu hanu ba: Martanin 'yan Najeriya bayan dage dokar Twitter

Dama bamu hanu ba: Martanin 'yan Najeriya bayan dage dokar Twitter

  • Dage dokar Twitter ya jawo hankalin jama'a bayan da gwamnati ta hakura da kanta ta cire dokar a jiya Laraba
  • 'Yan Najeriya sun yi martani, sun ce dama su basu daina yin Twitter ba, gwamnatin ne dai ta dakata da yin Twitter
  • Wasu da dama sun yi martani, wannan yasa muka tattaro kadan daga cikin martanin jama'a bayan dage Twitter

Najeriya - A jiya Laraba ne gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin kamfanonin sadarwa su bude kowa ya ci gaba da amfani da shafin Twitter a Najeriya bayan kwanaki 222 da dakatar dashi.

Dakatarwar dai ta biyo bayan dambarwar da aka samu tsakanin gwamnatin Najeriya da Twitter kan wani rubutu na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A baya gwamnatin Najeriya ta ba da wasu ka'idoji da tace dole Twitter ta cika su kafin daga bisani a bata damar ci gaba da gudunar da ayyukanta a Najeriya.

Kara karanta wannan

FG ta bayyana sharudda 5 da ta gindaya wa Twitter kafin dage dokar haramci

Martanin 'yan Najeriya kan dawo da Twitter
Dama bamu hanu ba: Martanin 'yan Najeriya bayan dage dokar Twitter | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Hakazalika, 'yan gwagwarmaya da masana tattalin arziki sun yi ta korafi kan dakatarwar, inda suke ganin bai kamata gwamnatin ta dakatar da dandalin na sada zumunta ba.

To, yanzu Twitter ya dawo bayan cika ka'idoji, to amma ya 'yan Najeriya suka ji? sannan meye martaninsu? Legit.ng Hausa ta tattaro kadan daga maganganun 'yan Najeriya.

Martanin 'yan Najeriya a shafin Twitter

Yayin da Legit.ng Hausa ta ziyarci dandalin Twitter, ta ga yadda batu kan dakatarwar Twitter ya dauki hankali matuka.

Wani gogaggen dan jarida a Najeriya mazaunin Turai, @gimbakakanda ya yi martani da cewa:

"Abin da #TwitterBan ya samar shine rufe bakin masu goyon bayan gwamnati tare da samar da wani salon magana wanda ya nuna gwamnati ba ta da masu kare mutunta.

Kara karanta wannan

Kamfanonin Sadarwa sun budewa yan Najeriya Tuwita bayan umurnin Buhari

"Na tabbata wadanda suka fito da ra'ayin sun yi tunanin za su cutar da 'yan kasa na yau da kullum. Dabaru ce mai matukar muni."

@realosuofia yace:

"Na dawo Najeriya tunda an cire dokar #TwitterBan.
"Na gode sosai Windscribe."

@FS_Yusuf_ ya ce:

"Mutane ba su bar Twitter ba, gwamnati ne ta yi hakan. Don haka suna bukatar jama'a don zabe, shi ya sa suke dage dokar #TwitterBan
"Wannan gwamnati ta san mahimmancin Twitter ga zabe. Kada ku bari kowa ya yaudare ku. APC na son manhajar fiye da yadda kuke tunani."

@Elitecapone1 ya ce:

"Sun cire kansu daga dakatarwar da suka sa wa kan ne #TwitterBan dai kamar ba su san cewa muna amfani da Twitter ba."

A wani labari, a watan Yunin shekarar da ta gabata, gwamnati ta sanar da dakatar da Twitter a Najeriya bayan kafar sada zumuntar ta goge wallafar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya ke barazanar magance 'yan awaren IPOB a yaren da suke ganewa.

Kara karanta wannan

Kaduna: Iyaye da malamai sun yi martani kan aikin kwana 4 na makarantun gwamnati

Wata uku da suka gabata, shugaban kasan ya bayar da umarnin dage Twitter, matukar sun cika sharuddan da aka sanya musu, TheCable ta ruwaito.

Wasu daga cikin sharuddan sun hada da yin rijista aiki a shari'ance, biyan haraji da kuma kiyaye dokokin haramta wallafa kamar yadda dokokin Najeriya suka tanadar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel