Kamfanonin Sadarwa sun budewa yan Najeriya Tuwita bayan umurnin Buhari

Kamfanonin Sadarwa sun budewa yan Najeriya Tuwita bayan umurnin Buhari

Yan Najeriya da dama a ranar Alhamis sun bayyana cewa lallai sun samu shiga shafin Tuwita ba tare da amfani da VPN ba bayan Gwamnati ta dage takunkumin da ta sanya tun bara.

Hakazalika Legit.ng Hausa ta gwada shiga Tuwita ba tare da VPN ba kuma ya bude.

Bayan watanni bakwai, Gwamnati tace a bude Tuwita

Gwamnatin tarayya ta dage dakatar da ayyukan kafar sadarwar Twitter a Najeriya bayan amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, The Cable ta rahoto.

Shugaban Kwamitin Fasaha na Najeriya kan hulda da Twitter da Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi, CCIE ne ya sanar da matakin dage dokar.

Gwamnatin tarayya ta dakatad da Tuwita a watan Yunin 2021 bayan tuhumar manhajar da yada labaran karya da jawaban batanci da ka iya haddasa rikici tsakanin yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Dama bamu hanu ba: Martanin 'yan Najeriya bayan dage dokar Twitter

Gwamnatin ta bayyana hakan ne yan kwanaki bayan kamfanin Tuwita ya cire jawabin Shugaban kasa.

Daga baya gwamnati tace sai kamfanin Tuwita ya cika wasu sharruda kafin a dage takunkumin.

Bayan kimanin watanni shida, Ministan Labarai Lai Mohammed, ya ce Tuwita ya cika sharudan da gwamnati ta gindaya kuma ana gab da dage takunkumin.

Kamfanonin Sadarwa sun budewa yan Najeriya Tuwita bayan umurnin Buhari
Kamfanonin Sadarwa sun budewa yan Najeriya Tuwita bayan umurnin Buhari
Asali: UGC

Martanin yan Najeriya

Aminu A M Koki yace:

"Kwarai da gaske amman nasha tambayoyi kafin komai ya dai-daita Alhamdulillah"

Farouq Bin Farouq:

"Har mun Dora daga inda aka tsaya"

Asali: Legit.ng

Online view pixel