Wayyo: Barawo mai imani ya ci karo da jakar kudi, bai tafi da komai ba sai N1800 na auno masara

Wayyo: Barawo mai imani ya ci karo da jakar kudi, bai tafi da komai ba sai N1800 na auno masara

  • Malam Bashir Aliyu Limanci ya nuna wata wasika da wani ya rubuta masa da ya tsinci alabensa
  • Wannan Bawan Allah ya bada labarin abin da ya faru tsakaninsa da mai tsintuwarsa a Facebook
  • Wanda ya tsinci alaben ya yi niyyar tafiya da ita, sai ya ga katin ATM don haka ya dauki N1800 rak

Kano - Wani Bawan Allah mai suna Bashir Aliyu Limanci ya bada labarin yadda ya jefar da alabensa, har kuma wani mutumi maras hali ya tsinta.

Malam Bashir Aliyu Limanci yace akwai katin ATM da kusan N9, 000 a cikin alaben (jakar kudin) a lokacin da abin ya faru, amma ba a dauke duka kudin ba.

Da yake magana a shafinsa na Facebook, Bashir Aliyu Limanci yace wanda ya tsinci jakar ya bar sa da wata wasika a takarda da za ta ba mutane tausayi.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba

Wannan barawo yake cewa ya na kallo jakar ta fado daga aljihun Bashir Limanci, kuma ya yi niyyar ya yi gaba da ita, amma sai ya iske katin ATM hudu.

A cewar wannan mutum mai tsintuwa a wasikar da ya bari, ganin akwai dukiya da abubuwa masu amfani a alaben, ya ga idan ya dauke jakar bai kyauta ba.

Barawo mai imani
Alaben Bashir Limanci Hoto: smith.almusawi/nairametrics
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kayi hakuri na dauki N1, 8000

Saboda gudun ya jefa mai alaben a mawuyacin hali, sai ya dawo da jakar dauke da duk abubuwan da ke ciki, amma ya zari N1800 daga kusan N10000 da ya tsinta.

Kamar yadda ya rubuta a wasikar da ya ajiye, wannan mutumi yace zai yi amfani da kudin da ya dauka ne domin ya saye masarar da zai samu ya ci da iyalinsa.

Wannan maras karfi mai imani ya rantse cewa an yi kwanaki har biyu a gidansa ba a ga abinci ba, sannan kuma ya na da yarar da yake daukar dawainiyarsu.

Kara karanta wannan

Talaka ya tsinci katuwar wayar salula, ya dawo da ita, ya nemi a ba shi tukwucin N1500 kacal

“ Don Allah ka gafarce ni, na dauki N1800 na saye masara saboda Wallahi kwana biyu ban kai komai gida ba, kuma ina da yara, Nagode” - Mai tsintuwa

Ina ma haka barayin gwamnati ke yi

Babban malamin nan, Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya yi magana game da wannan lamari mai ban al’ajabi, yace ina ma haka barayin gwamnati ke yi.

“Ina ma barayin alkalami a kasar nan irin wannan satar suke yi; su dan yakushi iya bukatarsu su da iyalansu su dawo mana da saura a dan yi mana aiki mu bayin Allah talakawa!
"Ai da mun ce da su masu imani ko cikin darasin da zamu dauka a cikin wannan kissa watakila akwai cewa, wasu masu yin laifi ba da zabinsu ne ba. Haka kuma ya zama wajibi mu duba irin halin da muka kai a kasa mai tarin arziki irin Najeriya.”

Kara karanta wannan

Yadda magidanci ya kashe matarsa da duka bayan sun samu sabani a Nasarawa

Ya tsinci waya ya yi cigiya

Kun ji labarin wani talaka a kasar Kenya da ya tsinci katuwar wayar salula, ya dawo da ita, ya nemi a ba shi tukwucin N1500 kacal duk da cewa bai da kudin kirismeti.

Wannan ya faru ne a lokacin da ake ganin cewa an daina yin tsintuwa a wannan zamanin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel