Talaka ya tsinci katuwar wayar salula, ya dawo da ita, ya nemi a ba shi tukwucin N1500 kacal

Talaka ya tsinci katuwar wayar salula, ya dawo da ita, ya nemi a ba shi tukwucin N1500 kacal

  • A lokacin da ake bikin kirismeti, Washington Ndegwa ya jefar da wayar shi yayin da yake wajen aiki
  • Ndegwa ya gano hakan ne bayan wani lokaci, don haka ya yi tunanin cewa wayar ta tafi kenan
  • Abin mamaki da Washington Ndegwa ya kira layinsa sai ya ji wanda ya tsinci wayar ya na magana

Kenya - Wasu su na cewa da wahala mutum ya jefar da abu, kuma ya ji an yi cigiya a kasar Kenya. Sai dai ba duka mutanen Duniya aka taru, aka zama daya ba.

An tabbatar da cewa har gobe akwai mutanen kwarai yayin da wani mutumi ya nuna tsabar gaskiya inda ya dawowa wani mutum wayarsa da ya tsinta.

Wani rahoto da Legit.ng ta samu ya bayyana cewa wannan mutumi mai gaskiya ya ci karo da waya mai ‘dan karen-tsada, amma ya nemi mai ita.

Kara karanta wannan

Cin amana: Ango ya kama amaryarsa da kwarto bayan kwana 9 da aurensu

A ranar bikin kirismetin 2021, tsautsayi ya fadawa Washington Ndegwa tun da dama bai wuce ranarsa, ya jefar da wayar salularsa yana wajen kai sakonni.

Ba a cire rai

Tun da an ce ka da mutum ya cire tsammani, sai Mista Ndegwa ya tuntubi wani abokin aikinsa, ya karbi aron wayarsa domin ya kira layin wayarsa da ta fadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Washington Ndegwa
Mista Washington Ndegwa Hoto: @Washington Ndegwa
Asali: Facebook

Kiran Ndegwa ke da wuya, sai ya ji wani mutumi ya dauki wayar, yace yana ta jiran kiran na sa.

“Na nemi wani abokin aikinmu, na ba shi labarin abin da ya faru domin ya taimaka mani da wayarsa, yace mani ya jefar da wayoyinsa da dama."
“Ina kira sai wani ya dauki wayar, ya fada mani cewa ya na tsammanin mai wayar ya kira lambar domin ya maido masa wayarsa, na ce ‘Ikon Allah!’”

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan sanda sun shiga tsakani yayin da kwarto ya kashe mijin daduronsa

Ya nemi tukwuici

Kamar yadda aka rahoto Ndegwa ya bada labari, wannan mutumi ya fadi inda za a hadu da shi.

Da Washington Ndegwa ya hadu da wanda ya tsinci wayar ta sa, sai ya bukaci ya taimaka masa da KSh 400 (N1,453.72) domin bai da abin da zai yi kirismeti.

Shi kuma saboda irin na sa alherin, sai ya cire har KSh 1000 (N3,634.29), ya ba wannan Bawan Allah da nufin yi masa godiya domin samun irinsa da wahala.

An kama barawon waya

A makon nan ne aka ji cewa Rundunar ‘yan sanda a jihar Yobe ta kama wani Usman Ali wanda ya gawurta wurin satar wayoyin mutane a garin Damaturu.

'Yan sanda sun dade su na neman wannan mutum da ake zargin ya saci wayoyi sama da 200. Sai wannan karo dubunsa ta cika bayan ya shiga gidajen mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel