Zaben 2023: Takalman Da Peter Obi Ya Saka A Kamfen Dinsa Na Imo Ya Haddasa Cece-kuce

Zaben 2023: Takalman Da Peter Obi Ya Saka A Kamfen Dinsa Na Imo Ya Haddasa Cece-kuce

  • Yanayin shigar Peter Obi a gangamin kamfen dinsa na jihar Imo ya ja hankalin mutane da dama a soshiyal midiya
  • Wani mai amfani da Twitter da ya bi kwakkwafin takalman Obi a yayin gangamin ya gano cewa sun yi butu-butu da kura
  • Mutane da dama sun so wallafar, suna masu cewa hakan ya nuna tsohon gwamnan na Anambra mutum ne mai saukin kai da kaunar jama'a

Imo - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, yana nuna saukin kansa a duk inda ya ce, hatta ga wajen yakin neman zabensa.

Yanayin shigar Obi a yayin gangamin yakin neman zabensa a Owerri, babban birnin jihar Imo a ranar Talata, 6 ga watan Disamba ya ja hankalin yan Najeriya da dama a soshiyal midiya.

Peter Obi
Zaben 2023: Takalman Da Peter Obi Ya Saka A Kamfen Dinsa Na Imo Ya Haddasa Cece-kuce Hoto: @VictorIsrael_.
Asali: Twitter

Lamarin ya fara ne lokacin da wani dan Najeriya mai suna @VictorIsrael_ drew ya mayar da hankalinsa kan takalman tsohon gwamnan na jihar Anambra a wajen gangamin.

Kara karanta wannan

Dole Ta Yi Masa? Ango Ya Yi Jugum Yana Kallon Amaryarsa Yayin da Take Girgijewa Ita Kadai A Bidiyo

A wallafar da yayi kan Twitter a ranar Talata, matashin ya ce yanayin kurar da takalman dan takarar na LP ya yi sun tabbatar da cewar shi na mutane ne kuma babu lokacin ado.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya rubuta:

"Na bi kwakkwafin takalman Peter Obi. Wannan mutumin na shiga kwatami kamar mu. Babu lokacin ado. Idan kace kana jin raradin da mutane ke ji, ka nuna mana cewa kana jin radadinsu. Owerri, jihar Imo. Muna godiya Obideints."

Jama'a sun yi martani

Yan Najeriya da dama da suka yi martani sun bayyana ra'ayoyinsu a Twitter, suna masu cewa Obi ne yafi dacewa da talakawa.

@ChineduNevo1:

"Wannan ya aika muhimmin sako."

@okoyekelvin10:

"Na ga takalmin nan, jikina yayi sanyi, kamar wani irin dan siyasa ne wannna? Ya sha banban sosai da wadanda muka sani...Allah ya taimake mu, don muna bukatar Obi fiye da yadda yake bukatarmu."

Kara karanta wannan

Siyasa Ba Hauka ba ce, Peter Obi ya Fadi Dalilinsa na Mutunta ‘Dan takaran PDP, Atiku

@hon__kelvin:

"Muna da taurin kai a kasar nan...Ban taba ganin mutum irin OBI ba a rayuwata mutumin nan ya yiwa kasar nan tsafta da yawa."

@AWorking9ja:

"Peter Obi...Yana tafiya kan takalman dan Najeriya mai rufin asiri.
"Ya fahimci radadinsu kuma yana da mafita ga matsalolin Najeriya.
"Mu zabi @PeterObi don zama shugaban kasa a 2023."

Baba-Ahmed ya zargi APC ba bata Peter Obi a idon arewa

A wani labarin, Datti Baba-Ahmed ya zargi APC da yan takararta da bata sunan Peter Obi a idon yan arewa da Musulmai.

Dan takarar mataimakin shugaban kasar na Labour Party ya ce sabanin abun da ake fadi, Obi na kaunar yan arewa matuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel