Hotuna yayin da babbar masarauta a Arewa ta nada fitacciyar jarumar fim a matsayin sarauniya

Hotuna yayin da babbar masarauta a Arewa ta nada fitacciyar jarumar fim a matsayin sarauniya

  • Masarauta a jihar Nasarawa ta nada wata jarumar fim a matsayin sarauniya a wata masarauta da ke fadar jihar
  • An nada ta ne bayan duba da kwazonta a matsayin mai kishin karfafawa mata, kamar yadda masarautar ta bayyana
  • Taron nadin sarautar ya samu halartar wasu fitattun mutane a kasar nan, ciki har da 'yan majalisu da dai sauransu

Nasarawa - Shahararriyar 'yar wasan kwaikwayo a Najeriya, Tayo Sobola, wacce aka fi sani da Sotayo Gaga, ta karbi kambun sarauta a jihar Nasarawa, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Jarumar, a ranar Juma’a, ta zama sabuwar Sarauniya (Queen Mother), ta Masarautar Uke, a wani gagarumin biki da ya samu halartar manya a jihar Nasarawa.

Sobola, ta bi sahun irin su D’banj, Omotola Jalade-Ekeinde, Tonto Dikeh, Ngozi Ezeonu, Amechi Muonagor da Genevieve Nnaji, wadanda aka baiwa mukaman sarauta a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Shekaru kadan bayan nada shi sarauta, fitaccen basarake ya riga mu gidan gaskiya

Yayin da sabuwar sarauniyar ke jawabi
Hotuna yayin da babbar masarauta a Arewa ta nada fitacciyar jarumar fim a matsayin sarauniya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Taron ya samu halartar fitattun mutane irinsu Tonto Dikeh, Femi Adebayo, socialite, T-pumpy, wasu 'yan majalisa da dai sauransu.

A jawabinta na karrama nadin da aka mata, jarumar ta godewa mutanen Uke bisa wannan karramawa.

Ta ce:

“Ina alfahari da cewa a matsayina na Bayarbiya ina nan ina rike da sandar masarautar Uke domin hakan na nuni cewa da'awar Najeriya daya da hadin kai tana aiki. A matsayinna na Sarauniya, yanzu fadar za ta fara ganin tasirin mata wajen yanke shawara da sauransu."

Da yake bayar da hujjar yanke shawarar nada jarumar a masarautarsa, Sarkin Uke, Abdullah Hassan, ya ce kishinta na karfafa mata bai tashi a banza ba.

Ya kuma bayyana cewa 'yar uwar mahaifinsa da suke tagwaye ita ce Sarauniya ta farko tun daga sheakarar 1970.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta fadi adadin 'yan ta'adda da ta hallaka a 2021, da yadda ta yi hakan

Ya ce, tun daga lokacin, babu wacce ta sake zama sarauniya a Uke.

A sakon da ya aike wa jarumar, Sarkin ya ce:

“Ina taya ki murna da kika kasance mafi karancin shekaru a cikin masu sarautar sarauniya a masarautar Arewa. Yana da kyau a lura cewa bayar da mukamin shi ne na biyu a tarihin masarautar”.

Kalli hotunan nadin sarautan

Nadin sarautar sarauniya a Nasarawa
Hotuna yayin da babbar masarauta a Arewa ta nada fitacciyar jarumar fim a matsayin sarauniya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hotunan nadin sarautar sarauniya a Nasarawa
Hotuna yayin da babbar masarauta a Arewa ta nada fitacciyar jarumar fim a matsayin sarauniya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hotunan nadin sarautar sarauniya a Nasarawa
Hotuna yayin da babbar masarauta a Arewa ta nada fitacciyar jarumar fim a matsayin sarauniya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wacece wannan jarumar?

Jarumar ta yi karatun digiri a Jami’ar Olabisi Onabanjo inda ta yi digiri a fannin shari’a da kuma Jami’ar Jihar Legas inda ta yi digiri a fannin harkokin gwamnati.

Jarumar ta fara harkar nishadantarwa ta hanyar fitowa a cikin bidiyon wakoki. Ta yi fice a fina-finan Yarbanci da Ingilishi sama da 70.

Wasu daga cikin shahararrun ayyukanta sun hada da Idakeji Ife, Egan, Corper Jide, Bella, Ojuloge Obinrin, Arewa Onijogbon, da dai sauransu.

Emeka Okoro ne ya gabatar da ita ga harkokin wasan kwaikwayo wanda aka ruwaito ya nuna mata hanyar shiga kungiyar 'yan wasan kwaikwayo ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta faɗi babban kalubalen da ya dagula mata lissafi a 2021

A wani labarin, mai sharhin labaran wasanni, Suo Chapele, ta bayar da labarin yadda ta karya wani babban tarihin shekaru dari na al'adar kasar Urhobo yayin da ta samu sarauta.

A wallafar da ta yi a shafinta na kafar sada zumunta na Instagram, Suo ta sanar da yadda sarakunan Urhobo ba su bai wa diya mace gadon sarautar mahaifin ta amma 'yan uwanta da dattawa suka ga ta dace da sarautar.

A yayin wallafa bidiyon ta sanye da kayan sarautarsu ta gargajiya, ta ce:

"A kusan shekaru dari, sarakunan Urhobo ba su bai wa 'ya mace gadon sarautar mahaifin ta ballantana idan akwai 'ya'ya maza. A yau, jama'a ta, 'yan uwa, da dattawa sun ga cancanta ta."

Asali: Legit.ng

Online view pixel