Latest
Kwamitin binciken da gwamnan jihar Anambra ya kafa ya tabbatar da cewa, Mmesoma Ejikeme ta jirkita sakamakon jarabawar JAMB da ta zauna a watan Mayu, 2023.
Hukumar 'yan sandan jihar Legas ta yi nasarar kama Amarah Kennedy, mutumin da ake zargi da yada hotuna marasa kyau na tsoffin yan matansa a soshiyal midiya.
Mahaifin jaririn da ƴan bindiga suka halaka mahafiyarsa a jihar Niger ya bayyana halin da suka tsinci jaririn a ciki. Ya ce sun samu zuma lulluɓe da jikinsa.
Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu yayin da 'yan sanda suka tare su a kauyukan karamar hukumar Ɗanja ta jihar Katsina, sun ƙashe guda 1.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka ƴan bindiga mutum.huɗu a jihar Zamfara tare da ceto mutum 24 da aka yi garkuwa da su a wani sumame da suka kai.
Shugaban kasa Bola Tinubu zai bar Najeriya gobe zuwa taron ECOWAS. A wajen wannan zama ne ECOWAS za ta tattauna a kan shirin kafa kudi da bunkasa kasuwanci.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yeriman Bakura ya ce jahilci da talauci ne suka haddasa matsalar tsaron 'yan bindigan daji a arewacin Najeriya.
Mataimakin shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya gana da mambobin tsohuwar majalisar dattawa ta 9 a fadar shugaban kasa ranar Jumu'a 7 ga watan Yuli.
Babbar kotun tarayya da ke Kano ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano daga gayyatar tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan bidiyon dala
Masu zafi
Samu kari