Yanzu Yanzu: Kotu Ta Dakatar Da Gayyatar Da Aka Yi Wa Ganduje Kan Bidiyon Dala

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Dakatar Da Gayyatar Da Aka Yi Wa Ganduje Kan Bidiyon Dala

  • Babbar kotun tarayya ta dakatar da hukumar PCACC daga gayyata ko cin zarafin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje
  • Hukumar yaki da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano ta gayyaci Ganduje domin ya amsa mata wasu tambayoyi dangane da bidiyoyinsa na dala
  • Tun a 2017 ne dai wani bidiyo ya bayyana inda aka zargi tsohon gwamnan da karbar cin hanci daga wajen wasu yan kwangila a lokacin yana kan karagar mulki

Kano - Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafe ta jihar Kano (PCACC) daga gayyata ko cin zarafin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje kan bidiyon da ake zarginsa da karbar dala.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hukumar PCACC a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, ta sanar da cewar ta gayyaci tsohon gwamnan don ya amsa wasu tambayoyi kan binciken da take yi a kan bidiyon wanda ake zarginsa da karbar cin hanci daga dan kwangila.

Kara karanta wannan

Ta Bayyana: Tambuwal, Yari, Wammako Da Wasu Tsaffin Gwamoni 11 Da Ke Karbar Fanso Bayan Zama Sanatoci

Abdullahi Ganduje
Yanzu Yanzu: Kotu Ta Dakatar Da Gayyatar Da Aka Yi Wa Ganduje Kan Bidiyon Dala Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Ganduje ya nemi kotu ta hana kamawa ko tsare shi

Sai dai a wata kara da aka shigar gaban mai shari'a A.M. Liman, a ranar Juma'a, 7 ga watan Yuli, tsohon gwamnan ya bukaci kotun da ta dakatar da wanda ake kara na takwas daga cin zarafi, tsoratarwa da gayyatar mai karar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka kuma an bukaci kotun da ta dakatar da wanda ake karar daga yin barazanar kamawa da tsare wanda ke karar ko yaransa ko wani danginsa ko kuma wani da ya yi aiki karkashin gwamnatinsa ko kuma kwace kadararorinsa ko na yaransa ko danginsa ta karfin tuwo.

Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta sammaci Ganduje

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje domin ya yi masu bayani kan bidiyoyinsa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Dala: Gwamnati Ta Janye Ƙarar da ta Haramtawa EFCC Binciken Ganduje

PCACC na shirin tsitsiye tsohon gwamnan domin ya amsa mata wasu tambayayoyi a kan bidiyon da ake zarginsa da karbar daloli daga hannun wasu yan kwangila a jihar.

Shugaban hukumar yaki da rashawa, Muhuyi Magaji Rimingado ya tabbatar da sahihancin bidiyoyin bayan binciken kimiyya ya nuna ba na bogi bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel