Mmesoma: “Ya Kamata Najeriya Ta yi Taka-tsan-tsan Kar Ta Halakar Da Ita", Keyamo Ya Yi Gargadin

Mmesoma: “Ya Kamata Najeriya Ta yi Taka-tsan-tsan Kar Ta Halakar Da Ita", Keyamo Ya Yi Gargadin

  • Tsohon minista, Festus Keyamo (SAN), ya kare dalibar nan da ta kara maki a Jamb dinta, Mmesoma Ejikeme
  • Keyamo ya ce ya kamata a ba yarinyar yar shekaru 19 da ta aikata almundahana shawara, a gyara mata kuskurenta sannan a sanyata a hanya madaidaiciya
  • Keyamo ya bayyana cewa ya kamata a bari Mmesoma ta samu gurbin karatu daidai da makinta na ainahi

Nnewi, jihar Anambra - Wani jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli cewa ya kamata a bari Mmesoma Ejikeme, dalibar da ta kara maki a jarrabawarta na JAMB ta samu gurbin karatu a jami'a.

Legit.ng ta rahoto cewa a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Keyamo ya ce abun da Mmesoma ke bukata a yanzu shine nasiha, gyara da kuma jagoranci.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗalibar da Ta Kara Makin JAMB Ta Tona Asiri, Ta Yi Bayanin Abinda Ta Aikata Dalla-Dalla

Festus Keyamo da Mmemoma Ejikeme
Mmesoma: “Ya Kamata Najeriya Ta yi Taka-tsan-tsan Kar Ta Halakar Da Ita", Keyamo Ya Yi Gargadin Hoto: Augustine Onyekachukwu Ike, Festus Keyamo, ESQ
Asali: Facebook

"Mmesoma na da hazaka", Festus Keyamo

Hukumar zana jarrabawa ta JAMB ta ce ta haramtawa dalibar wacce aka zarga da kirkirar sakamakon UTME na 2023 yin jarrabawa na tsawon shekaru uku. Sai dai kuma Keyamo ya nuna adawa da haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta a shafin nasa:

"Da gangan na jira har sai an kai karshen binciken nan kafin na yi martani a kan wannan lamari mai cike da takaici na diyarmu, Mmesoma Ejikeme.
"Yarinya ce mai hazaka, duba ga ainahin makin da ta samu na 249. Ya kamata kasar ta yi taka-tsan-tsan don kada ta yi mata illa. Abun da take bukata shine nasiha, gyara da jagoranci. Shakka babu bata san nauyin abun da take aikatawa ba. A matsayin matasa, yawancinmu mun yi kura-kuran da ba a taba saninsu ba.
"Ya kamata iyayen sun karfafa mata gwiwar fitowa bainar jama'a don baiwa JAMB hakuri, yan uwanta da yan Najeriya sannan bayan nan a barta ta samu gurbin karatunta da ainahin makin da ta samu."

Kara karanta wannan

Kwamitin Bincike Ya Bayyana Abinda Yakamata Ya Faru Da Mmesoma Ejikeme Bayan Ta Kara Makin JAMB

Bugu da kari, tsohon ministan ya yi gargadin cewa duk wanda ke kokarin kawo wani bayani na daban kan wannan lamari baya taimakonta da yan uwanta.

Ya kare zancensa da cewa:

"Lokaci ya yi da za rufe babin wannan abun takaicin sannan a ci gaba da harka. Wannan shine rokona."

Kwamitin bincike ya tabbatar da Mmesoma ta kara makinta ne na JAMB

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kwamitin binciken da gwamnatin jihar Anambra ta kafa ya tabbatar da cewa ɗalibar nan da ake zargi, Mmesoma Ejikeme, ta yi maguɗin sakamakon JAMB/UTME.

Jaridar Punch ta tattaro cewa kwamitin, wanda gwamna Charles Soludo, ya kafa da nufin gano gaskiya, ya ce aihinin makin da ɗalibar ta ci shi ne 249 ba 362 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel