Kwamitin Anambra Ya Tabbatar da Laifin Mmesoma Na Kara Makin JAMB

Kwamitin Anambra Ya Tabbatar da Laifin Mmesoma Na Kara Makin JAMB

  • Kwamitin da gwamnan Anambra ya kafa domin gano gaskiya kan ruɗanin sakamakon jarabawar Ejikeme Joy Mmesoma ya gama aikinsa
  • A rahoton da kwamitin ya miƙa wa Soludo, ya ce ɗalibar ta ƙara wa kanta maki ta hanyar amfani da wayar hannu
  • Ruɗanin sakamakon Mmesoma ya ja hankalin mutane da dama a Najeriya bayan JAMB ta sanar da gaskiyar abinda ya faru

Anambra - Kwamitin binciken da gwamnatin jihar Anambra ta kafa ya tabbatar da cewa ɗalibar nan da ake zargi, Mmesoma Ejikeme, ta yi maguɗin sakamakon JAMB/UTME.

Jaridar Punch ta tattaro cewa kwamitin, wanda gwamna Charles Soludo, ya kafa da nufin gano gaskiya, ya ce aihinin makin da ɗalibar ta ci shi ne 249 ba 362 ba.

Mmesoma Ejikeme da gwamnan Anambra.
Kwamitin Anambra Ya Tabbatar da Laifin Mmesoma Na Kara Makin JAMB Hoto: Professor Charles Soludo
Asali: Facebook

Gwamnan ya kafa kwamitin ranar Laraba kuma ya ɗora masa nauyin gudanar da binciken kwakwaf kan ruɗanin da ya haɗa hukumar JAMB da Mmesoma.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Yi Kus-Kus da Wasu Jiga-Jigai a Aso Villa, Ya Roƙi Alfarma 1 Tal

Mmesoma, ɗalibar makarantar sakandiren Anglican, ta zana jarabawar shiga manyan makarantu UTME wacce hukumar JAMB ke shiryawa a watan Mayu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai idai ɗaliban ta tsinci kanta a matsayin abin zargi da ake bincike bayan ta ayyana cewa ta samu maki 362, wanda daga bisani JAMB ta ce sakamakon bogi ne.

Abinda kwamitin ya gano kan ruɗanin sakamakon JAMB

The Cable ta tattaro cewa kwamitin ya miƙa rahoton bincikensa mai shafi 6 ga gwamna Charles Soludo, kuma kwamishinan yaɗa labarai, Sir Paul Nwosu, ya raba wa manema labarai ranar Jumu'a.

Ya ce ya tattauna da ɓangarori daban-daban tun da Mmesoma, jami'an hukumar JAMB da sauran masu hannu a lamarin har da shugaban makarantar sakandiren Anglican.

Wani ɓangaren rahoton binciken kwamitin ya ce:

"Sakamakon da hukumar JAMB ta saki dangane da jarabawar da ɗalibar nan, Mmesoma Ejikeme, ta zana shi ne maki 249."

Kara karanta wannan

Tirƙashi: An Ba Daliba Mafi Hazaƙa a Jarabawar JAMB Kyautar Kuɗi Har Naira Miliyan 2.5

"Haka nan sakamakon farko da ɗalibar ta nuna wa duniya cewa ta ci 362 na bogi ne ƙarya ne kuma cike yake da rashin gaskiya tun daga lambar rijista, ranar haihuwa, sunan cibiya da sauransu."
"Ɗalibar da bakinta ta amince cewa ta jirkita sakamakon ta kirkiri na bogi da hannunta ta hanyar amfani da waya. Shugaban makarantar da sakataren ilimin yankin sun yi takaicin abinda ta aikata."

Gwamnan Taraba Ya Ayyana Ilimin Firamare da Sakandire Kyauta a Jiharsa

A wani labarin na daban kuma Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya ya maida karatun makarantar Firamare da Sakandire kyauta.

Ya ce wannan na ɗaya daga cikin alkawurran da ya ɗauka lokacin kamfe, bayan haka zai rage raɗafin cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel