Tsohon Sanatan APC Ya Garzaya Kotu Domin Hana EFCC & AGF Bincike a Kan Shi

Tsohon Sanatan APC Ya Garzaya Kotu Domin Hana EFCC & AGF Bincike a Kan Shi

  • Muhammed Adamu Bulkachuwa ya dumfari kotu saboda a tsaida hukumomi daga bincikensa
  • Tsohon Sanatan na Jihar Bauchi ya roki kotun tarayya ta ba shi kariya daga EFCC, DSS, NPF da AGF
  • Bulkachuwa ya kafa hujja da dokar da ta hana a bibiya abin da Sanatoci su ka aikata a Majalisa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Muhammed Adamu Bulkachuwa wanda ya wakilci Arewacin Bauchi a Majalisar dattawa ya tafi kotu domin hana ayi bincike game da shi.

The Cable ta kawo rahoto cewa tsohon Sanatan ya bukacikotun tarayya da ke garin Abuja ta hana hukumar ICPC binciken kalaman da ya yi a majalisa.

Da yake jawabin ban-kwana a majalisar tarayya, Muhammed Adamu Bulkachuwa ya nemi ya jefa mai dakinsa watau Zainab Bulkachuwa a cikin matsala.

Muhammed Adamu Bulkachuwa
Sanata Muhammed Adamu Bulkachuwa Hoto: @GeoffreyOnyeama
Asali: Twitter

Wasu sun ce Sanatan ya nuna Mai shari’a Zainab Bulkachuwa ta rika amfani da matsayinta a kotun daukaka kara domin yin hukunci na son kai.

Kara karanta wannan

"Tun Asali Abu 2 Ke Ya Kawo 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya" Tsohon Gwamna Ya Fasa Ƙwai

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Leadership ta ce Bulkachuwa ta rike shugabancin kotun daukaka kara tun daga 2014 har zuwa 2020 da tayi ritaya bayan da ta cika shekaru 70 a Duniya.

Bulkachuwa ya kai hukumomi kotu

Daga cikin wadanda Sanata Bulkachuwa ya yi kara a kotu akwai babban lauyan gwamnati, akawun majalisar tarayya da kuma jami’an tsaro na DSS.

Shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/895/2023 ta hada da ‘yan sanda da hukumar ICPC.

Jaridar take cewa Bulkachuwa ya na so sashe na I na dokar majalisa ta 2017 ta haramta yib bincike a kan duk abin da ya fada cikin zauren majalisa.

A cewar tsohon ‘dan majalisar na Bauchi, akwai dokar da ta ba duk wani ‘dan majalisa garkuwa, ta hana hukuma ta bibiyi abin da ya yi a wajen aiki.

‘Dan siyasar ya kuma roki kotun tarayyar ta ayyana cewa bai halatta jami’an ICPC su gayyace shi domin yin jawabi kan abin da ya wakana a majalisar ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Abin da Ya Gagari Buhari, Ya Sasanta Rikicin Hukumomi 2 a Cikin Wata 1

Zuwa yanzu kotu ba ta fara sauraron karar Bulkachuwa da hukumomin gwamnatin tarayyar ba.

Silvio Berlusconi ya bar Daloli

Rahoto ya zo cewa a kasar Italiya, Marigayi Silvio Berlusconi da ya rasu kwanan nan ya bar dukiyar da ta fi karfin Naira Tiriliyan 5 a asusun bankinsa.

Bazawarar da za tayi wa tsohon Firayim Ministan takaba watau Marta Fascina mai shekara 30 za ta samu fiye da Naira Biliyan 80 a matsayin gadonta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel