Latest
Za a ga sunayen manyan ‘yan siyasa da Bola Tinubu ya manta da su wajen nada Ministoci. Akwai ‘yan siyasar Kano; Rabiu Musa Kwankwaso, Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnatin jihar Kano ta hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ya jihar ta damƙe uba da ɗansa bisa zargin hannu a badaƙalar wawure Naira Biliyan Huɗu.
Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Agusta idan Gwamnatin Tarayya ba ta janye karar da ta shigar da kungiyar ba.
Sojin sama sun yi luguden wuta kan 'yan bindiga tare da kashe manyansu biyu da suka hada da Ado Aliero da Dankarami a wani hari da suka kai a jihar Zamfara.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zaɓo sama da minista ɗaya a cikin jihohi tara domin majalisar dattawa ta tantance su tare da amincewa da su zama ministoci.
Femi Fani-Kayode da Festur Keyamo (SAN) sun goyi bayan zabin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ministocin rukuni na biyu, sun ce baki ɗayansu sun cancanta.
Ƙungiyar fulani makiyaya ta ƙasa (MACBAN) ta yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa yayanta a muƙaman gwamnati ko da kuwa na shara ne a Aso Villa.
Shugabannin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas sun bayyana cewa ko ƙaɗan tsohon gwamna Nyesom Wike bai taimaki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ɓa a zaben 2023.
Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki kauyukan jihar Neja inda suka halaka mutum daya tare da sace mutane fiye da 50 a kananan hukumomin Munya da Rafi da ke jihar.
Masu zafi
Samu kari