Jerin Jihohin Da Shugaba Tinubu Ya Zabo Ministoci Guda 2

Jerin Jihohin Da Shugaba Tinubu Ya Zabo Ministoci Guda 2

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zaɓo aƙalla minista ɗaya daga kowace jiha cikin jihohi 36 da birnin tarayya Abuja, bayan ya miƙa jerin sunayen ministocinsa kashi na biyu ga majalisar dattawa a ranar Laraba, 2 ga watan Agustan 2023.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ƙarin ministocin 19 ya sanya yawan ministocin da Shugaba Tinubu ya naɗa ya kai jimillar mutum 47, cewar rahoton The Punch.

Jihohin da suka samu minitoci 2
Jihohi tara ne suka samu ministoci 2 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/ Hon Aliyu Usman/@muhammadpate
Asali: UGC

Sai dai, wasu jihohin sun samu minista sama da guda ɗaya. Hakan baya rasa nasaba da gudunmawar da suka ba Shugaba Tinubu wajen lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

A satin da gabata ne dai Shugaba Tinuɓu ya fara aikewa da sunayen ministoci 28 ga majalisar dattawa domin tantancewa, sannan ya ƙara aikewa da ragowar ministoci 19 a wannan satin, wanda hakan ya sanya ministocin suka zama 47.

Kara karanta wannan

Jiga-Jigan APC 2 Kuma Makusantan Tinubu Sun Yi Magana Bayan Rashin Ganin Sunayensu a Jerin Ministoci

Ga jerin jihohin da suka samu sama da minista ɗaya a nan ƙasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihar Katsina ta samu ministoci 2

Ahmad Dangiwa - Jihar Katsina

Hanatu Musa Musawa - Jihar Katsina

Tinubu ya zaɓo mutum 2 ƴan asalin jihar Cross River domin zama ministoci

John Enoh - Jihar Cross River

Betta Edu - Jihar Cross River

Jihar Bauchi ta samu ministoci 2

Yusuf Maitama Tuggar - Jihar Bauchi

Ali Pate - Jihar Bauchi

Jihar Ogun ta samu ministoci 3

Dr. Bosun Tijjani - Jihar Ogun

Dr. Ishak Salako - Jihar Ogun

Olawale Edun - Jihar Ogun

Jihar Legas ta samu gurbin ministoci 2

Tunji Alausa - Jihar Legas

Lola Ade John - Jihar Legas

Tinubu ya zaɓo ministoci 2 daga jihar Kebbi

Kara karanta wannan

Binani, Keyamo, Fashola Da 'Yan Siyasa 10 Da Ba Su Da Rabon Zama Ministoci

Dr Yusuf Tanko Sununu - Jihar Kebbi

Atiku Bagudu - Jihar Kebbi

Tinubu ya ba jihar Kano gurbin ministoci 2

Abdullahi Tijjani Gwarzo - Jihar Kano

Dr. Maryam Shetti - Jihar Kano

Jihar Niger ta samu ministoci 2

Mohammed Idris - Jihar Niger

Sanata Aliyu Sabi Abdullahi - Jihar Niger

Taraba ta samu gurbin ministoci 2 a wajen Shugaba Tinubu

Uba Maigari Ahmadu - Jihar Taraba

Sani Abubakar Danladi - Jihar Taraba

'Yan Siyasa Da Ba Su Samu Minista Ba

A wani labarin kuma, wasu jiga-jigan ƴan siyasa da suka wahalta wajen samun nasarar Shugaba Tinubu, an yi ba su a wajen rabon ministoci.

Ƴan siyasan dai sun bayar da gudunmawa a wajen nasarar Shugaba Tinubu, daga cikinsu akwai Aisha Dahiru Binani da Festus Keyamo.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel