Latest
Wani magidanci Ojo Olaoye, ya roki wata kotun gargajiya da ke Oja Oba, Mopa a Ibadan, jihar Oyo da ta raba aurensa mai shekaru 51 da matarsa Janet Olaoye.
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya samu kansa a cikin cakwakiya bayan an nuna bidiyonsa yana umartar sarakunan gargajuya su tashi tsaye su gaida shi.
Bola Tinubu ya zakulo Tope Fasua, ya aika shi ofishin Kashim Shettima a matsayin mai bada shawara. Fasua ya ce ai hidimtawa Ubangijinsa da matsayin.
Abdul-Samad Rabiu BUA, shugaban rukunin kamfanonin BUA ya ce kamfaninsa na siminti na kokarin ganin ya karya farashin siminti a Najeriya zuwa N3,500.
Manoma sun shiga tsahin hankali a wasu ƙauyuka akalla 15 da ke jihar Taraba biyo bayan ayyukan 'yan bindiga wanda ya tilasta musu hakura da amfanin gonakinsu.
Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Mista Lucky Aiyedatiwa, ya nesanta kanaa da wata takardar murabus da ake yaɗawa cewa ya yi murabus daga kan muƙaminsa.
Gwamnan jihar Filato, Celeb Muftwanga, ya naɗa masu taimaka masa na musamman 136 a faɗin kananan hukumomin jihar 17 kuma zasu soma aiki nan take.
Shugaba Tinubu ya nada Muhammad Sani Dattijo, babban yaron tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin CBN.
Shugaban kasar Faransa ya ce a yanzu haka sojin Jamhuriyar Nijar sun yi garkuwa da jakadan kasar, tare da hana kai masa abinci a ofishin jakadancin kasar.
Masu zafi
Samu kari