Lauya Ya Maida Martani Ga Tinubu Kan Nada Gwamnan Babban Banki CBN

Lauya Ya Maida Martani Ga Tinubu Kan Nada Gwamnan Babban Banki CBN

  • Lauya mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Festus Ogun, ya ayyana matakin shugaba Tinubu ya naɗa sabon gwamnan CBN da saɓa doka
  • Ya ce Bola Ahmed Tinubu ba shi da ikon naɗa gwamnan CBN yayin da har yanzu ba a cire Emefiele da aka dakatar ba ko ya yi murabus
  • A ranar Jumu'a, Bola Tinubu ya amince da naɗa Olayemi Cardoso tare da mataimakan gwamna 4 gabanin majalisa ta tantance su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Wani lauya a Najeriya, Festus Ogun, ya caccaki shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa naɗa Dokta Olayemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Masanin dokokin ya soki matakin shugaban ƙasar ne a shafinsa na manhajar X (watau Tuwita a baya) ranar Jumu'a, 14 ga watan Satumba, 2023.

Shugaba Tinubu da dakataccen gwamnan CBN.
Lauya Ya Maida Martani Ga Tinubu Kan Nada Gwamnan Babban Banki CBN Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Godwin Emefiele
Asali: Facebook

Lauyan ya bayyana naɗin Dokta Cardoso a matsayin sabon gwamnan CBN da wanda ya saɓa wa doka da kuma yi wa kundin tsarin mulki hawan ƙawara.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Sanya Labule Da Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

Idan baku manta ba a ranar Jumu'a (Jiya) shugaba Tinubu ya amince da naɗin Cardoso da mataimakan gwamnan CBN guda huɗu da zaran majalisar dattawa ta tantance su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya saɓa wa doka - Ogun

Da yake maida martani, Mista Ogun ya ce bai dace Tinubu ya nada Cardoso ba yayin da har yanzu ba a kori Godwin Emefiele, gwamnan CBN da aka dakatar ba, kuma bai yi murabus ba.

"Nada sabon Gwamnan CBN a lokacin da "Gwamnan CBN da aka dakatar" tun da farko ba a tsige shi ba, kuma bai yi murabus ba, ya sabawa doka da kundin tsarin mulki."

Idan zaku iya tuna wa, shugaba Tinubu ya dakatar Emefiele daga matsayin gwamnan CBN, kuma awanni bayan haka hukumar tsaron farin kaya ta damƙe shi.

Har yau Emefiele na hannun DSS kuma babu wani sahihin bayani da ya nuna ya yi murabus daga muƙaminsa na gwamnan CBN ko kuma an tsige shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabon Gwamnan Babban Banki CBN da Mataimaka 4

Gwamnan Jihar Filato Ya Nada Sabbin Hadimai 136 a Gwamnatinsa

A wani rahoton na daban Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya amince da naɗa sabbin hadimai 136 a matsayin mambobin majalisar zartarwa.

Gwamnan ya bayyana haka ne da daren ranar Jumu'a, 15 ga watan Satumba, 2023 a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Gyang Bere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel