Latest
A ranar 11 ga watan Nuwamba za a fafata tsakanin 'yan takarkari a jihar Kogi da su ka hada da Dino Melaye da Usman Ododo da Ajaka da Leke da sauransu.
Dakarun tsaron haɗin guiwa sun shiga cikin daji sun farwa yan bindigan daji a jihar Kebbi, sun samu nasarar kashe ɗaya kuma suka ceto mutane uku.
Wani jirgin ruwa da ya ɗauko mafi akasari mata da kananan yara ya gamu da hatsari a yankin ƙaramar hukumar Ovia ta kudu maso yamma a jihar Edo ranar Alhamis.
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bai wa kotun koli shawarar yin azumin kwanaki uku don gano gaskiyar takardun Tinubu ma su cin karo da juna.
Bidiyon wani bikin aure da ya yadu ya jefa mutane cikin rudu da fargaba a lokaci guda. Masu amfani da soshiyal midiya na jiyewa amaryar tsoron abun da ke tinkarota.
Ministan Abuja ya dage wajen ganin yadda za a tara kudin shiga. Nyesom Wike ya na so a tabbatar da dokar haraji ta na aiki a Abuja, hakan zai kai mutane kurkuku.
Al'umma su na faman kokawa a game da 'dan karen tsadar rayuwa. Man fetur ya na cigaba da kara tsada a Najeriya duk da kamfanin NNPCL ya musanya zargin rashin kaya.
Gwamnati na kokarin hana Dala cigaba da tashin kullum-yaumin. Dalar Amurka ta dade da haura N1000 a kasuwar canji, Edun ya shaida cewa ana fama da karancin kudi.
Dauda Lawal ya fito da bayanai da za su gaskata zargin da yake yi wa Bello Matawalle. An tona yadda Matawalle ya yi bindiga da dukiyar Zamfara a aikin filin jirgi.
Masu zafi
Samu kari