Jerin ’Yan Takarar Zaben Gwamnan Jihar Kogi 5 da Za a Fafata da Su a Watan Nuwamba

Jerin ’Yan Takarar Zaben Gwamnan Jihar Kogi 5 da Za a Fafata da Su a Watan Nuwamba

Yayin da zaben jihar Kogi ke kara karatowa akwai wasu batutuwa da yawa da ke da tasiri a zaben da su ka hada da yare da kuma yanayin yanki da sanuwa.

Mutanen Igala da ke mazabar Gabashin jihar sun mulki jihar har na tsawon shekaru 20 duk da haka su na son kari.

Igala sun fi ko wane yare sanuwa a jihar inda su ka mamaye kananan hukumomi tara daga cikin 21 na jihar.

Jerin 'yan takarar da za su fafata a zaben gwamnan jihar Kogi
Cikakken Sunayen ’Yan Takarar Zaben Gwamnan Jihar Kogi 5. Hoto: Melaye, Ododo, Murtala.
Asali: Twitter

Sannan akwai Ibira da su ke son kawo magajin Gwamna Yahaya Bello, Usman Ododo daga Kogi ta Tsakiya don samun tsawon shekaru dai dai da na Igala a mulki.

Har ila yau, akwai Okun da ke mazabar Kogi ta Yamma wadanda har zuwa yanzu ba su samu damar mulkar jihar ba tun bayan kirkiro jihar.

Kara karanta wannan

Satar Mazakuta: Menene Gaskiyar Batun Da Ya Zama Ruwan Dare a Sassan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit ta jero muku manyan ‘yan takara da za su fafata a zaben:

1. Leke Abejide

Dan takarar jam'iyyar ADC, Leke Abejide
Dan takarar jam'iyyar ADC. Hoto: Elder Leke Abejide.
Asali: Twitter

Ajibede a yanzu haka shi ne mamban majalisar Tarayya a mazabar Yagba wanda ya na daya daga cikin wadanda za a fafata da su a zaben.

Dan takarar na jam’iyyar ADC ya yi kaurin suna a yankin wurin biya wa dalibai kudin jarrabawar WAEC tun bayan zuwanshi majalisar.

2. Dino Melaye

Dan takarar jam'iyyar PDP, Dino Melaye
Dan takarar jam'iyyar PDP, Dino Melaye. Hoto: Dino Melaye.
Asali: Twitter

Melayi wanda dan jam’iyyar PDP ne na daya daga cikin wadanda su ke gaba-gaba a wannan zaben da za a gudanar a watan Nuwamba.

Tsohon sanatan da ke wakiltar Kogi ta Yamma ya tsaya a takarar gwamna na fidda gwani inda ya sha kaye a hannun Injiniya Musa Wada a shekarar 2019.

3. Usman Ahmed Ododo

Dan takarar jam'iyar APC, Usman Ododo
Dan takarar jam'iyar APC, Usman Ododo. Hoto: Usman Ododo.
Asali: Twitter

Ododo shi ne dan takarar jam’iyyar APC wanda Gwamna Yahaya Bello ya zaba kuma ya ke marawa baya.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tsageru sun yi yunkurin kashe gwamnan APC a Arewa, bayanai sun fito

Ya kasance a cikin siyasar jihar tsundum tun bayan nada shi a matsayin Odita-Janar na jihar a shekarar 2016.

4. Murtala Yakubu Ajaka

Ajaka shi ne dan takarar jam’iyyar SDP wanda ya fito daga yankin Kogi ta Gabas, ya na da magoya baya daga dukkan kananan hukumomi duk da matsalolin da ya samu.

Ajaka shi ne tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC kafin dakatar da shi a matsayin dan jam’iyyar.

5. Usman Jibrin

Jam’iyyu akalla kusan 10 ne su ka mara masa bayan wanda dan jam’iyyar AP ne da ke da magoya baya musamman mutanen Igala.

Jibrin wanda tsohon sojan ruwa ne, ya mulki jihar Arewa maso Tsakiya a mulkin Janar Murtala Mohammed a shekarar 1975 zuwa 1977.

Gwamna Bello ya musanta kai masa hari

Kun ji cewa, Gwamna Yahaya Bello ya musanta cewa an kai masa farmaki a kan hanyar Abuja.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: 'Yan sanda sun kame wadanda ake zargi da shiga gida tare da kashe dattijuwa a Gombe

An yi ta yada cewa wasu da ake tunanin ‘yan bindiga ne sun farmaki tawagar motocin gwamnan a kan hanyar Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel