Latest
An gano rikicin siyasar jihar Ribas yana da nasaba da matakin da Gwamna Siminalayi Fubara ya dauka na farfado da manufar Rotimi Amarchi, wannan ya fusata Wike.
Wata matar aure ta haifi tagwaye kasa da awanni 24 bayan mijinta ya mutu. Bidiyon matar da yaran nata ya tsuma zukatan mutane da dama a soshiyal midiya.
Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar kamo daliban firamare 2 da suka cinna wa makarantarsu wuta a jihar Ogun, rundunar ta ce ta fara bincike kan wannan danyen aiki.
Kotun daukaka kara reshen Abuja ta tabbatar da Natasha Akpoti-Uduagan a matsayin sahihiyar yar takarar da ta lashe zaben sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya.
Hukumar NEMA ta bayyana cewa a halin yanzu an ceto mutane 12 da ransu yayin da wasu 17 suka mutu a haɗarin jirgin ruwan Taraba, an shiga kwana na uku.
Rundunar sojoji a jihar Kebbi ta yi ajalin wani kasurgumi kuma kwamandan 'yan bindiga, Mainasara da wasu biyu a jihar Kebbi a wani mummunan hari da ta kai.
Dauda Lawal Dare ya ce gwamnatin da ta shude ta Bello Matawalle ta saci kudi ta hanyar biya kusan duka kudin kwangilar a lokacin da ba a kai ga fara ayyukan ba.
Wani mutum da tsinci teba a kwali maimakon wayar iPhone 15 ya koka cikin kunar rai yayin da yake dudduba kwalin. Bidiyon ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.
Tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar PDP a jihar Kogi, Joseph Erico, ya jagoranci dandazon masu sauya sheka daga jam'iyyu sun rungumi APC mai mulki.
Masu zafi
Samu kari