Mutum 17 Sun Mutu Yayin da Wasu 12 Suka Tsallake Rijiya da Baya a Hatsarin Jirgi a Arewa

Mutum 17 Sun Mutu Yayin da Wasu 12 Suka Tsallake Rijiya da Baya a Hatsarin Jirgi a Arewa

  • Hukumar NEMA ta bayyana cewa an ceto mutane 12 yayin da wasu 17 suka mutu a haɗarin jirgin ruwan da ya afku a jihar Taraba
  • A ranar Asabar da ta gabata ne jirgin ruwan da ya ɗauko ƴan kasuwa galibi mata da ƙananan yara 104 ya kife a tekun Benuwai
  • A halin yanzu, daraktan NEMA ya ce an yi wa waɗanda suka mutu jana'iza a bakin kogin bayan amincewar danginsu

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta ce jami’an ceto sun gano gawarwaki 17 bayan da wani jirgin ruwa dauke da mutane 104 ya kife a jihar Taraba.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, NEMA ta ƙara da cewa jami'ai sun kuma ceto mutane 12 da ransu daga cikin ruwan.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: An Gano Gawarwakin Mutane Sama da 70 a Ƙaramar Hukuma Ɗaya Tal, Gwamna Ya Magantu

Halin da ake ciki bayan jirgin ruwa ya kife da mutane sama da 100 a Taraba.
Hadarin Jirgin Taraba: An Ceto Mutane 12 Yayin da Wasu 17 Suka Mutu Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Jirgin ya kife ne a ranar Asabar tare da mutane sama da 100 galibi ’yan kasuwa da suka hada da mata da yara da suka dawo daga kasuwar kifi ta Mayorenero da ke ƙaramar hukumar Ardo/Kola.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haɗarin ya afku ne yayin da jirgin ruwan ya kama hanyar zuwa garin Binnari a ƙaramar hukumar Karim Lamido jihar Taraba.

Da yake hira da BBC Hausa ranar Litinin, Daraktan sashin aikin agaji na hukumar NEMA, Bashir Garga, ya ce har yanzu ana ci gaba da aikin ceto.

Yadda aka yi musu jana'iza

Jirgin ruwan ya nutse ne a tafkin Benue kuma an shiga kwana na uku kenan na aikin ceto mutane sama da 100 da ibtila'in ya rutsa da su.

Tuni dai aka binne wasu daga cikin wadanda suka mutu a bakin kogi a Mayoreneyo da Binnari.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace babban malamin addini da wasu mutum 2 a Taraba

Muƙaddashin shugaban safarar ruwa a Taraba, Jidda Mayoreneyo, ya ce an yi jana’izar shida daga cikin wadanda suka rasu kashe a jiya a garin Mayoreyo.

A cewarsa, iyalan mamatan ne suka bada izinin a musu jana'iza, sauran kuma an binne su a Binnari ranar Asabar.

Jidda ya bayyana cewa gawarwakin mutum huɗu da aka ƙara tsamo wa an binne su a bakin Kogin bayan danginsu sun amince da haka.

Dirama tsakanin mata da miji a Kotu

A wani rahoton na daban Wata matar aure mai suna, Zainab Bello, ta buƙaci Kotu ta raba aurenta ta hanyar Khul'i, ta ce a shirye take ta maida wa mijin sadakin da ya biya.

Magidancin, Nura Ashiru, ya faɗa wa Kotu cewa idan har matar tana.son saki to ta ba shi Naira miliyan 1.5 saboda ɓarnar da ta masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel