Zaben Gwamnan Bayelsa: Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Matsayin Takarar Timipre Sylva Na APC

Zaben Gwamnan Bayelsa: Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Matsayin Takarar Timipre Sylva Na APC

  • Sansanin jam'iyyar APC na jihar Bayelsa ya ɓarke da murna gabanin zaɓen gwamnan jihar da za'a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba
  • Kotun daukaka kara da ke Abuja warware hukuncin babbar kotu na haramtawa Timipre Sylva ɗan takarar APC yin takara a zaɓen gwamnan Bayelsa
  • Kotun ta ce babbar kotun tarayya da ke Abuja ba ta da hurumin saurare da hukunci kan ƙarar da aka shigar a kan Sylva

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun daukaka ƙara da ke Abuja, ta warware soke zaɓen Timipre Sylva, a matsayin ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Fubara da Ministan Abuja sun haɗu a Aso Villa ana ƙishin-kishin ɗin Tsige Gwamnan PDP

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, alƙalin kotun ya ce babbar kotun tarayya da ke Abuja ba ta da hurumin saurare da hukunci a ƙarar da Demesuoyefa Kolomo ya shigar.

Kotun daukaka kara ta warware hukuncin hana Sylva takara
Kotun daukaka kara ta warware hukuncin hana Timipre Sylva takara a zaben gwamnan Bayelsa Hoto: Timipre Silva/Court of Appeal
Asali: Facebook

Kotun mai alƙalai uku ta yi hukunci cewa, kasancewarsa ba ɗan takara ba a zaɓen fidda gwani na gwamna na jam'iyyar APC ba, Kolomo bai da hurumin tuntubar kotun domin ƙalubalantar zaɓen ɗan takarar gwamnan jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta yi watsi da hukuncin babban kotun tarayya, ta amince da ɗaukaka ƙarar da Sylva ya shigar, ta kuma ta ba da dukkanin buƙatun da ya nema, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Kotun ta amince da buƙatun Sylva da APC

Kotun dai ta amince da duk wasu buƙatun da aka nema sannan ta kuma bayar da N1m ga Sylva a matsayin diyya.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya faɗi ƙungiyoyin 'yan ta'adda 2 da ke barazanar shafe Najeriya

A wani hukunci na daban, kotun ta kuma amince da irin wannan ɗaukaka ƙara da jam’iyyar APC ta shigar a kan wannan batu tare da bayar da diyyar N1m ga APC.

APC Ta Yi Martani Kan Cire Sunan Sylva

A wani labarin kuma, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bayelsa, ta yi martani kan cire sunan ɗan takararta, Timipre Sylva, daga cikin sunayen ƴan takarar gwamnan jihar.

Jam'iyyar ta yi nuni da cewa wannna wani koma baya ne na wucin gadi, sannan ta buƙaci magoya bayanta da su kwantar da hankulansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel