Latest
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikata. Gwamna Radda zai rika biyan albashin N70,000.
Wasu yan jam'iyyar PDP sun ga ta kansu yayin aka ki karbarsu a APC bayan sun sauya sheka a jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya makwanni kadan bayan gudanar da zabe.
Kungiyar ICNGO ta karrama karamin ministan tsaro, Dakta Bello Matawalle. Kungiyar ta karrama ministan ne kan nasarorin da ya samu a wajen samar da tsaro.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ta samar da isassun kudi a bangaren tatara bayanan sirri domin daƙile duk wata baranar tsaro idan ta taso a jihar.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta yi doguwar tattaunawa da ƴan bindiga kafin su tuba su ajiye makamansu a yankin Birnin Gwari.
Kungiyar matasan Arewa ta bayyana cewa har yanzu yankin na matakin tattaunawa kan sake zaɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a 2027 ko juya masa baya.
Gidauniyar Abdullahi Ganduje ta bude sabon masallacin Juma'a da makarantar Islamiyya domin koyar da addini a karamar hukumar Takai da ke jihar Kano.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya ce ko sisin kwabo na gwamnati ba su yi ciwo ba wajen jawo hankalin ƴan bindigar da suka ajiye makamao a jihar ba.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka ya yi murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya inda ya ce ya hakura da siyasa gaba daya.
Masu zafi
Samu kari